Nijeriya Amurka Kasuwanci

Ƙarin harajin Amurka ya janyo koma-baya a fitar da kayayyakin Najeriya

Ƙarin harajin da gwamnatin Trump ta ƙaƙaba ya janyo raguwar fitar da kayayyakin Najeriya zuwa Amurka, tare da ƙaruwa sosai a shigo da kayayyaki daga can.

Newstimehub

Newstimehub

22 Dec, 2025

indir e1766392252605

Najeriya ta yi asarar kusan naira biliyan 940.98 a fitar da kayayyaki zuwa Amurka a cikin watanni tara na farkon shekarar 2025, biyo bayan ƙarin harajin da shugaban ƙasar, Donald Trump, ya ƙaƙaba, kamar yadda bayanan Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) suka nuna. Rahoton NBS ya bayyana cewa daga watan Janairu zuwa Satumba na 2025, Najeriya ta fitar da kayayyaki zuwa Amurka na kimar naira tiriliyan 3.65, ƙasa da naira tiriliyan 4.59 da aka fitar a daidai wannan lokaci a shekarar 2024.

Wannan ya nuna cewa an samu raguwar kashi 20.5 cikin ɗari a fitar da kayayyakin. An bayyana cewa wannan koma-baya ya faru ne a lokacin da gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da sabon tsarin haraji, inda Shugaba Donald Trump ya ƙara harajin kayayyakin Najeriya daga kashi 14 zuwa 15 cikin ɗari. Sabon harajin ya fara aiki ne a ranar 7 ga Agustan 2025, kuma ya fi shafar kayayyakin da ba na man fetur ba da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka.

A gefe guda kuma, shigo da kayayyaki daga Amurka zuwa Najeriya ya ƙaru sosai, inda ya kai naira tiriliyan 6.80 daga naira tiriliyan 3.01, wanda ke nuna ƙarin kashi 125.5 cikin ɗari. Wannan yanayi ya nuna cewa a shekarar 2025, Najeriya ta shigo da kayayyaki daga Amurka fiye da yadda ta fitar mata.

Majiyar Labari: BBC Hausa