An naɗa Burhanettin Duran a matsayin shugaban Hukumar Sadarwa ta Turkiyya

Duran ya maye gurbin Fahrettin Altun, wanda ya sauka daga muƙaminsa bayan kusan shekara bakwai a kujerar, inda a yanzu ya karɓi wani sabon aiki a matsayin shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan’adam.

Newstimehub

Newstimehub

11 Jul, 2025

cc9a3c0b0e21be2c12ea0f498dd5172c77c4ed1fc05468822d97c824e1c79915

An nada Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Burhanettin Duran a matsayin sabon Daraktan Sadarwa na Ƙasar, bisa ga wata sanarwa daga Shugaban Ƙasa da aka wallafa a cikin Jaridar Gwamnati a safiyar Alhamis.

Ya maye gurbin Fahrettin Altun, wanda ya riƙe wannan muƙamin tun daga ranar 25 ga Yulin 2018, a yanzu kuma an naɗa shi a matsayin shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan’adam da Daidaito ta Turkiyya (TİHEK).

Duran ya kammala digirinsa na farko a Kimiyyar Siyasa da Dangantakar Duniya daga Jami’ar Bogazici, sannan ya samu digirin-digirgir (Ph.D.) a Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Bilkent.

Ya taba yin aiki a matsayin babban mai kula da cibiyar SETA Foundation, sannan aka nada shi cikin Kwamitin Tsaro da Siyasar Waje na Shugaban Kasa a shekarar 2018.

A watan Mayu na shekarar 2024, ya zama Mataimakin Ministan Harkokin Waje.

Altun ya tabbatar da barinsa wannan mukami da kuma sabon nadinsa ta hanyar wallafa wani sakon sada zumunta, inda ya nuna godiyarsa ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan saboda amincewa da goyon bayansa a tsawon kusan shekaru bakwai da ya yi yana aiki.

“Ina mika godiyata ta zuciya ga Shugaban Ƙasa wanda ya ba ni wannan dama, ga iyalina, ga abokan aikina wadanda suka yi aiki tukuru kan Tsarin Sadarwar Turkiyya, da kuma dukkan ‘yan jarida da suka tsaya tsayin daka wajen fafutukar gaskiya,” in ji shi.

Har ila yau, ya mika fatan alheri ga Duran, yana mai bayyana shi a matsayin “abokin aiki mai daraja kuma ɗan’uwa” wanda suka yi aiki tare na tsawon shekaru masu yawa.