Gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa an saki ragowar ɗalibai 130 na makarantar sakandaren St. Mary’s da ke Papiri a Jihar Neja, waɗanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a ranar 21 ga watan Nuwamba. Mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara na musamman kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga, ne ya wallafa hotunan ɗaliban a cikin motocin bas guda biyu a ranar Lahadi, a shafinsa na X. Onanuga ya bayyana cewa ana sa ran ɗaliban za su isa Minna, babban birnin Jihar Neja, a ranar Litinin.
Ya ƙara da cewa tuni an saki ɗalibai 100 a baya, lamarin da ya kai adadin ɗaliban da aka kuɓutar zuwa 230. A cewarsa, an saki ɗaliban ne sakamakon ƙoƙarin ɓangaren tattara bayanan sirri na rundunar sojin Nijeriya. Makonni biyu da suka gabata, gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya tarbi ɗalibai 100 na makarantar St. Mary’s, waɗanda ofishin mai bai wa Shugaban Nijeriya shawara kan sha’anin tsaro ya miƙa masa bayan an kuɓutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane.
A lokacin miƙa ɗaliban, Wing Commander Abdullahi Dare ya bayyana cewa ofishin mai bai wa Shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro ne, tare da haɗin gwiwar rundunar sojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro, suka gudanar da aikin kuɓutar da ɗaliban. A nasa jawabin, Gwamna Umar Bago ya nuna godiyarsa ga Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan sha’anin tsaro, da kuma dukkan jami’an tsaron ƙasar, tare da sauran masu ruwa da tsaki, bisa rawar da suka taka wajen kuɓutar da ɗaliban.
Tun da farko, ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), ta hannun shugabanta na reshen Jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna, ta bayyana cewa ba ta samu cikakken bayani a hukumance ba dangane da kuɓutar da ɗaliban. A ranar 21 ga watan Nuwamban 2025 ne wasu ‘yan bindiga, a kan babura, suka kai hari makarantar St. Mary’s Catholic School, inda suka sace mutum 315, ciki har da ɗalibai 303 da malamai 12.
Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro tare da mafarauta sun bazu a dazukan yankin domin nemo mutanen da aka sace. Daga bisani, hukumomin makarantar sun sanar da cewa aƙalla ɗalibai 50 sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane, inda suka samu damar komawa wurin iyayensu lafiya.
Majıyar Labari: Trt Hausa














