Gangamin ya nuna irin yadda mutane ke cike da tausayin Falasɗinawa, domin dubban mutane sun taru a birnin Istanbulsuna goyon bayan Gaza tare da kira da a kawo ƙarshen yaƙin da Isra’ila ke yi. Gangamin mai taken “Ba Za Mu Yi Shiru ba” – We Do Not Remain Silent ya samu halartar shugabannin addini, kungiyoyin fararen hula da masu fafutuka sama da kungiyoyi 400.
Masu gangamin sun fara ne da sallar asuba a manyan masallatai irin su Ayasofya Grand Mosque, Sultanahmet, Fatih, Suleymaniye da Eminonu Yeni Cami, kafin daga bisani su yi maci zuwa Gadar Galata, riƙe da tutocin Turkiyya da Falasɗinu. Sun riƙa ɗaukar alluna masu ɗauke da saƙonni kamar “Daga Istanbul zuwa Gaza, gaisuwa ga masu gwagwarmaya” da “A ‘Yanta Falasɗinu.”
Shugabannin ƙungiyoyi daban-daban sun yi jawabai, ciki har da Bilal Erdogan, inda suka jaddada goyon baya ga Falasɗinawa tare da yin addu’a domin samun ‘yanci da adalci a Gaza da Birnin Ƙudus. An kuma ga jama’a na raba shayi da simit ga mahalarta, yayin da jami’an tsaro suka tabbatar da zaman lafiya duk da cunkoson jama’a.
Masu gangamin sun ce saƙonsu na shekarar 2026 shi ne neman adalci, zaman lafiya da kare rayukan Falasɗinawa, suna mai cewa Istanbul ta aika da “babban saƙon goyon baya ga duniya.”
Majiyar Labari: TRT HAUSA














