Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana cewa a fili yake yanzu cewa ƙungiyar PKK/YPG ba ta yin sassauci ko sauya matsaya sai idan an matsa mata da ƙarfi, yana mai cewa tattaunawa kaɗai ba ta ishe su.
Da yake magana a wata hira kai tsaye da TRT Haber, Fidan ya ce ƙungiyar, wadda ya bayyana a matsayin reshen PKK, ba ta da ikon shiga sulhu ba tare da barazanar ƙarfi ba, musamman dangane da abubuwan da ke faruwa a Syria.
Ya zargi PKK/YPG da ɗaukar matsaya mai tsauri a kan gwamnatin Damascus, inda ya ce suna neman goyon bayan wasu ƙasashen waje ta hanyar fakewa da yaƙi da Daesh, tare da hulɗa da wasu ‘yan majalisar Amurka da kuma Isra’ila.
Fidan ya jaddada cewa wannan dabarar ba za ta kai su ga nasara ba, yana mai kira gare su da su nemi mafita ta gaskiya tare da manyan ‘yan wasan yankin. Ya kuma ce Turkiyya ta riga ta isar da wannan saƙo ta hanyoyin diflomasiyya da na tsaro, amma ba a samu sauyi ba.
A cewarsa, makomar yankin ita ce haɗin kai da gina ƙasa guda a Syria da ke bai wa kowa hidima ba tare da la’akari da ƙabila ba, yana mai cewa dole PKK/YPG ta bar matsayarta ta yanzu ta rungumi hanyar zaman lafiya da tattaunawa.














