Amurka Gabas Ta Tsakiya Zaman Lafiya

Iran: Trump ya wallafa bidiyon da ke cewa masu zanga-zanga sun karɓe Mashhad

Shugaban Amurka Donald Trump ya yada wani bidiyo da ke ikirarin cewa masu zanga-zanga sun karɓe birnin Mashhad a Iran, duk da cewa rahotanni masu zaman kansu ba su tabbatar da hakan ba.

Newstimehub

Newstimehub

9 Jan, 2026

download 7

Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Truth Social yana ikirarin cewa masu zanga-zanga sun karɓe iko da birnin Mashhad, na biyu mafi girma a Iran. Bidiyon, wanda ya fito daga tashar talabijin ta Isra’ila Channel 13, ya ce sama da mutane miliyan ɗaya ne suka mamaye birnin, tare da janye dakarun gwamnati.

Sai dai rahotanni masu zaman kansu ba su tabbatar da wannan ikirari ba, inda ba a samu shaida cewa jami’an tsaro sun fice daga Mashhad ko kuma cewa masu zanga-zanga sun karɓe cikakken iko da birnin ba. Mashhad dai birni ne mai yawan jama’a kusan miliyan huɗu, kuma yana ɗauke da hubbaren Imam Reza, wani muhimmin wurin ziyara ga Musulmi.

A baya, Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta iya tsoma baki idan gwamnatin Iran ta yi amfani da ƙarfi kan masu zanga-zangar lumana. Daga baya kuma, ya danganta mutuwar wasu mutane a yayin zanga-zangar da matsalar sarrafa taro da turmutsitsi, yana cewa ba a san wa za a ɗora laifi kai tsaye ba.

Gwamnatin Iran ba ta fitar da wata sanarwa ta hukuma kan adadin mutanen da suka mutu ko suka jikkata ba. Sai dai kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ce daruruwan ’yan sanda da mambobin ƙungiyar Bassidj sun jikkata. A gefe guda, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta HRANA ta ce an kashe mutane 42, an kama fiye da 2,200 tun bayan fara zanga-zangar.

Zanga-zangar ta fara ne a ƙarshen Disamba 2025 bayan ’yan kasuwa a Tehran sun nuna adawa da tabarbarewar tattalin arziki da faduwar darajar kuɗin ƙasar. Tun daga lokacin, gwamnati ta kakaba takunkumin Intanet, duk da haka hotuna da bayanai na ci gaba da fita zuwa waje.

Majiyar Labari: AA