Hukumar yawon buɗe ido ta ƙasar ta bayyana cewa a shekarar 2025 an samu zuwan kusan masu yawon buɗe ido miliyan 19.8, abin da ya kafa sabon tarihi ga masanan harkar. Wannan ya nuna ci gaba mai ƙarfi idan aka kwatanta da shekarar 2024, inda aka samu ƙaruwa da kashi 14%.
Ma’aikatar ta ce wannan sabon adadi ya tabbatar da cewa bangaren yawon buɗe ido na shiga sabon matakin cigaba. Ministar yawon buɗe ido, Fatima-Zahra Ammor, ta ce wannan ya nuna sauyi mai zurfi a tsarin yawon buɗe ido a ƙasar, tare da jin dadin jagoranci da hangen nesa daga Sarki Mohammed VI. Ta ce ɓangaren ya zama mai ɗorewa kuma mai alfanu ga al’umma.
A shekarar 2024, yawon buɗe ido shi ne tushen kudaden shiga na biyu mafi girma ga Maroko bayan kuɗaɗen da ‘yan Maroko mazauna ƙetare ke turo wa gida, inda aka samu masu yawon buɗe ido miliyan 17.4, kuma ta kasance kasar da ta fi jan hankalin masu yawon buɗe ido a Afrika.














