NCDC: Zazzaɓin lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya a 2025

Kazalika sanarwar ta ce kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar suna cikin jihohin Ondo da Bauchi da Edo da Taraba da kuma Ebonyi ne.

Newstimehub

Newstimehub

22 Jul, 2025

cb04cc9c9378f01ad97bebf3c0398bc8cc4befa038970e0103c29495c27614eb

Adadin mutanen da zazzaɓin lassa ya kashe a Nijeriya a wannan shekarar ta 2025 ya kai mutum 151, in ji hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasar (NCDC).

Wata sanarwa da hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin ta ce yawan kisan da cutar zazzaɓin lassa ke yi ya ƙaru daga kashi 17.3 cikin 100 na waɗanda suka kamu da ita a shekarar 2024 zuwa kashi 18.9 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar a shekarar 2025.

Sanarwar ta ce kwanan na an samu ƙarin mutum 11 da suka kamu da cutar a cikin jihohin ƙasar shida, lamarin da ya mayar da jimullar waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar a wannan shekarar mutum 800.

Kazalika sanarwar ta ce kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kamu da cutar suna cikin jihohin Ondo da Bauchi da Edo da Taraba da kuma Ebonyi ne.

Cutar zazzaɓin lassa dai tana yaɗuwa ne ta hanyar kashin ɓera, kuma cuta ce da ke iya yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.