Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama ma’aikatan jirgin ruwa Indiyawa 22 bayan gano hodar iblis (cocaine) mai nauyin kilogiram 31.5 a cikin jirgin MV Aruna Hulya, wanda ya iso daga Tsibirin Marshall a ranar 2 ga Janairu.
Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya tabbatar da cewa an cafke su ne a gaɓar ruwan Legas. Wannan na cikin jerin manyan kamen da NDLEA ke yi, bayan kama ‘yan Philippines 20 a watan Nuwamba da ake zargi da safarar cocaine daga Brazil, tare da ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin Amurka da Birtaniya wajen dakile shigo da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.














