Sojojin Rundunar Operation Hadin Kai sun cafke motocin a-kori-kura guda biyu da ake zargin suna jigilar kayayyaki zuwa ga ’yan ta’addar ISWAP a Jihar Borno. Rundunar ta ce ta samu nasarar ne bayan sahihin bayanan sirri daga jama’a game da motsin motocin daga Dapchi a Jihar Yobe zuwa yankin Magumeri na Borno.
A cewar mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Sani Uba, dakarun sun tare motocin a hanyar da aka gano za su bi, inda suka ƙwato kayayyaki da dama. Abubuwan da aka samu sun haɗa da motocin farar-hula biyu, safaya taya 31, rim ɗin mota 23, kekuna biyu, makullan mota 12, altaneta uku, buhunan gari, gawayi, doya, barguna, katifa, wayoyin hannu da kuma wasu kuɗaɗe.
Sani Uba ya jaddada cewa sojojin za su ci gaba da katse hanyoyin samar wa ’yan ta’adda kayayyaki da hana su ’yancin motsi, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.














