Yayin da rikicin Sudan ke ci gaba da raba dubban fararen-hula da gidajensu, Turkiyya ta fito fili ta yi Allah wadai da ta’addancin da mayaƙan Rundunar RSF ke aikatawa. A wani kira na gaggawa, Ankara ta bukaci a ba da damar kai agajin jinƙai ba tare da tangarda ba ga al’ummomin da rikicin ya fi shafa.
Da yake jawabi a taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sudan, wakilin Turkiyya Ahmet Yildiz ya ce ƙasar na Allah wadai da hare-haren RSF kan fararen-hula, tare da jaddada cewa Sudan yanzu ta zama mafi girman matsalar ‘yan gudun hijira a duniya. Ya bayyana baƙin cikin Turkiyya kan abubuwan da suka faru a Al Fasher da yankin Kordofan.
Yildiz ya kuma soki harin da RSF suka kai a ranar 13 ga Disamba kan sansanin samar da kayayyaki na rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Abyei, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Bangladesh shida tare da jikkata wasu takwas.
Ya jaddada cewa Turkiyya na goyon bayan cikakken ikon Sudan, haɗin kan yankunanta da ‘yancin kai, yana mai cewa hanya ɗaya tilo ta samun mafita ita ce tattaunawa da tsari na siyasa mai gaskiya. Ya kuma bayyana gudunmawar Turkiyya wajen kai kayan agaji sama da tan 10,000, kayan kiwon lafiya don yaki da kwalara, da tantuna 30,000.














