Ƙasashen yankin Gulf sun yi gargaɗi cewa za su iya ɗaukar mataki muddin aka ci gaba da yaƙin Iran, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, wanda ya bayyana ƙarin fargaba game da yiwuwar watsuwar yaƙin zuwa ƙasashen yankin.
Da yake magana bayan ya kai ziyara ƙasashen yankin waɗanda suka haɗa da Saudiyya, Qatar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Fidan ya shaida wa manema labarai a Ankara ranar Asabar cewa jami’an da ya gana da su — cikinsu har da waɗanda ya tattauna da su a Riyadh — suna gani za a ci gaba da yaƙin zuwa mako biyu ko uku, inda hatsarin yaƙin ke ƙaruwa.
Ya ƙara da cewa ƙasashen yankin Gulf sun bayyana ƙarara tun da farko cewa ba za su bari a yi amfani da sararin samaniyarsu ko sansanonin sojinsu domin kai hari kan Iran ba kuma ba za su shiga yaƙin ba.
A lokaci guda, sun zargi Iran da kai hare-hare da gangan kan cibiyoyin tsaro da wuraren fararen-hula da cibiyoyin tattalin arzikinsu.
‘Yaƙin yana iya daɗewa’
Fidan ya yi gargaɗin cewa yaƙin yana iya ɗaukar sabon salo, inda ya yi ishara game da alamun samun saɓani tsakanin Amurka da Isra’ila.
“Isra’ila za ta yi ƙoƙarin yaudarar Amurka sannan ta hana tsagaita wuta ko samar da zaman lafiya a nan kurkusa,” in ji shi. “Ana ta samun bayanai na saɓani game da manufar Amurka da kuma ta Isra’ila. Hakan zai iya sawa a tsawaita yaƙin.”
Ya ƙara da cewa babu yiwuwar tattaunawa a yayin da ake ci gaba da yaƙin, amma ya bayyana abin da mai yiwuwa zai faru: a tsagaita wuta ta ƙaramin lokaci wadda za ta buɗe hanyar tattaunawa, yayin da kuma za a iya samun wani gurbi na sabunta yaƙin idan hanyar diflomasiyya ta ci tura.
“Isra’ila za ta iya iya ɗaukar matakin tsawaita yaƙin domin yin gagarumar ɓarna kan Iran,” in ji Fidan, inda ya ce babban tarnaƙin shi ne rashin amincewa a yi tattaunawar zaman lafiya, ba kawai rashin tsarin kawo ƙarshen yaƙin ba.
Tattaunawa a Riyadh domin samun ‘matsaya iri ɗaya’
Fidan ya ce taron da aka yi ranar 19 ga watan Maris a Riyadh ya haɗa ƙasashen yankin waɗanda suke cikin yaƙin kai-tsaye da kuma waɗanda ba sa ciki, inda aka tattauna kan halin da ake ciki.
“An yi taron ne domin yin nazari kan bayanan kowace ƙasa ta yankin… an yi shi ne domi samun matsaya iri ɗaya,” a cewarsa, inda ya ƙara da cewa mahalarta taron sun amince da buƙatar gaggawa ta shawo kan halin da ake ciki.
Ya ce ko da yake taron ya mayar da hankali ne kan matakin Iran, amma Turkiyya ta bijro da rawar da Isra’ila take takawa a yaƙin, inda Ankara ta bayyana musamman shirin Isra’ila ci gaba da mamaya, kuma an saka wannan batu a sanarwar haɗin gwiwa ta bayan taro da aka fitar.














