Sojojin Nijeriya sun kama mutum uku da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda aikin masinja a Katsina

Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation Fansan Yamma, sun kama wasu mutane uku da ake zargi da yi wa ‘yan’tadda aikin masinja ta ha hanyar kai musu kuɗaɗen fansa da sauran kayayyaki.
26 Sep, 2026
An sake harbe wani ɗan Nijeriya har lahira a Afirka ta Kudu

Rahotanni sun ce an harbe mutumin ne a wata mashaya bayan wata gardama da aka yi da shi kan ko za a iya fitar da kofin gilas daga cikin mashayar zuwa waje.
25 Sep, 2026
Nijeriya ta buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro na MƊD

Jawabin na Shugaban, wanda Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gabatar, ya kuma yi kira da a ware kujeru biyar na wucin-gadi wa Afirka a Kwamitin Tsaron.
25 Sep, 2026
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma’adinai

Ministan Ma’adinan Ƙasa na Nijeriya, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, sun sanya hannu kan “tsarin zuba jarin Amurka a albarkatun ma’adinan Nijeriya da darajarsu ta kai dala biliyan 700” a New York.
24 Sep, 2026

Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai

Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa

Kalaman Malami da Fagbemi sun ci karo da juna kan yarjejeniyar sulhu ta $200m kan aikin Mambila

Gwamnatin Nijeriya ta bayar da wa’adin mako biyu don bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC

Manyan ’yan siyasar Nijeriya sun karkatar da miliyoyin dalolin gwamnati sun sayi gidaje a Amurka’
22 Sep, 2026
An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja
Masu zanga-zangar, daga ƙauyen Dekara da al’ummomin da ke makwabtaka da su a karamar hukumar Borgu sun taru a hedikwatar gwamnatin yankin da ke New Bussa don neman a saƙi wadanda aka yi garkuwa da su.

22 Sep, 2026
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce Shettima na da cikakken ikon wakiltar Tinubu a taron UNGA
Shugaba Tinubu ya bai wa Mataimakinsa Kashim Shettima umarnin wakiltarsa da kuma jagorantar tawagar Nijeriya a babban taron zauren MDD.

21 Sep, 2026
An kama mai PoS da ake zargi da aiki da taimakon mai garkuwa da mutane
Dakarun tsarin jihar Katsina ne suka kama Nasiru tare da: Abubakar Sayaya da Nura Baka Sati da kuma Ubale Mai Cange

21 Sep, 2026
‘Yanbindiga sun kashe mutum tara a jihar Filaton Nijeriya
‘Yan bindigar da ba a san su wane ne ba sun buɗe wuta bayan sun isa yankin Barkin Ladi, in ji rahotannin. An ji wa wasu ciwo a harin.

21 Sep, 2026
An tsare kwamandan NSCDC da wasu jami’an hukumar na jihar Neja kan mutuwar masu haƙar ma’adinai 37
Hukumar ta ce jami’ai 24 suna hannunta domin gudanar da bincike kan rawar da suka taka wajen mutuwar mutanen.

19 Sep, 2026
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin mutum 10 don binciken mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC a Neja
Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa wani kwamiti mai zaman kansa mai mambobi 10 domin binciken mutuwar mutane 37 da aka ruwaito sun mutu a lokacin da suke tsare a hannun jami’an NSCDC.

19 Sep, 2026
Waɗanda suka tsira a Jihar Neja sun bayyana yadda abokan sana’arsu suka rasu a ɗakin da aka tsare su
Wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 40 da aka wallafa a intanet, wanda aka ce yana nuna waɗanda abin ya rutsa da su a lamarin ranar Alhamis, ya nuna gawawwakin wasu da dama daga cikin samari sanye da gajerun wando kawai.

18 Sep, 2026
Ana zargin giya ta kashe mutum 49 a Jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya
Hukumomin Jihar Ondo na zargin cewa gubar methanol ce ta haddasa mutuwar mutanen, daga wata giya da ake hadawa a gargajiyance wadda aka fi sani da “Monkey Tail”.

18 Sep, 2026
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan NSCDC bisa mutuwar masu haƙar ma’adinai 37 a jihar Neja
Ibrahim ya ce gwamnatin jihar Neja ta soke gangamin yaƙin neman zaɓe na Jam’iyyar APC da aka shirya yi ranar Asabar, 19 ga watan Satumba, a Minna, babban birnin jihar, biyo bayan aukuwar lamarin.

17 Sep, 2026
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗau mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Ƙungiyar NLC, a wata sanarwar da shugabanta, Joe Ajaero, ya sanya wa hannu ranar Laraba ta ce a halin yanzu ana sayar da litar man fetur ne kan kuɗi naira 1,430 a muhimman birane.



