Nijeriya

‘Yan Nijeriya sun kashe Naira tiriliyan 6.6 kan sayen datar waya a cikin shekara ɗaya

An ƙididdige wannan adadi ne bisa bayanan yawan amfani da intanet da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta fitar, tare da amfani da matsakaicin ƙimar naira 431 kan kowane gigabyte (GB), ba wai bisa kuɗaɗen shiga da kamfanonin sadarwa suka bayyana ba.

Newstimehub

Newstimehub

11 Aug, 2026

11b7c3a2 e8ac 4322 b776 9ebbdbaa08e0 1786436316918

Kuɗin da ‘yan Nijeriya ke kashewa a kan amfani da intanet ya kai kimanin naira tiriliyan 6.6 a cikin watanni 12 da suka, abin da ke nuna girman tattalin arzikin dijital na ƙasar da ke ci gaba da faɗaɗa, duk da cewa kamfanonin sadarwa na fuskantar ƙarin kuɗaɗen gudanar da ɗimbin bayanan intanet da ake amfani da su.

An ƙididdige wannan adadi ne bisa bayanan yawan amfani da intanet da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta fitar, tare da amfani da matsakaicin ƙimar naira 431 kan kowane gigabyte (GB), ba wai bisa kuɗaɗen shiga da kamfanonin sadarwa suka bayyana ba.

Kafin ƙarin kuɗin sadarwa na kashi 50 cikin 100 da NCC ta amince da shi a watan Janairun 2025, matsakaicin farashin 1GB na data ta wayar hannu a Nijeriya ya kai kusan naira 287.50.

Bayan ƙarin kuɗin ya fara aiki a watan Fabrairun 2025, matsakaicin farashin da aka kayyade ya tashi zuwa naira 431.25 kan kowane 1GB, yayin da a zahiri farashin da ake sayar da data a kasuwa ya kasance tsakanin naira 475 da naira 637.50, gwargwadon kamfanin sadarwa da tsarin data da kwastoma ya zaɓa.

Bayanan NCC sun nuna cewa ’yan Nijeriya sun yi amfani da terabytes miliyan 15.32 na bayanan intanet tsakanin watan Yunin 2025 da Mayun 2026.

Idan aka mayar da wannan adadi zuwa gigabytes, ya zama kusan GB biliyan 15.32. A farashin naira 431 kan kowanne GB, hakan na nufin masu amfani da intanet sun kashe kimanin naira tiriliyan 6.6 wajen amfani da data.

Amfani da intanet ɗin bai taƙaita ga manyan kamfanonin sadarwa guda huɗu ba, wato Airtel, MTN, T2 da Globacom. Ya haɗa da amfani da intanet ta hanyar wasu kamfanonin da ke da lasisin samar da ayyukan sadarwa da fasahohi daban-daban, ciki har da GSM, layukan intanet na waya, masu samar da sabis na intanet (ISP) da kuma ayyukan VoIP.

Matsakaicin naira 431 da aka yi amfani da shi wajen ƙididdigar ba farashin da hukumar sadarwa baki ɗaya ta amince da shi ba ne. Farashin data da mutane ke biya a zahiri ya bambanta bisa kamfanin sadarwa, fasahar da ake amfani da ita, abokin ciniki, kunshin data, tayin rangwame, tsawon lokacin amfani da kunshin da sauran sharuddan kasuwanci.

A cewar bayanan NCC, yawan amfani da data a kowane wata ya ƙaru daga kusan terabytes miliyan 1.04 a watan Yunin 2025 zuwa tarihi mafi girma na terabytes miliyan 1.50 a watan Mayun 2026, wanda ke nuna ƙarin kusan kashi 44 cikin 100.

A tsawon wannan lokacin, yawan amfani da intanet ya kasance yana ƙaruwa gabaɗaya, duk da cewa an samu raguwar amfani a wasu watanni.

Amfani da data ya ƙaru zuwa kusan TB miliyan 1.13 a watan Yuli da TB miliyan 1.15 a watan Agusta, kafin ya tsaya kusan a matakin ɗaya a watan Satumba.

A watan Oktoba da Nuwamba, amfanin ya haura TB miliyan 1.2, sannan ya ƙaru zuwa TB miliyan 1.39 a watan Disamba.

Ƙarin nazarin bayanan ya nuna cewa amfani da data ya ci gaba da kasancewa a kusa da wannan matakin a watan Janairun 2026, kafin ya ragu zuwa kusan TB miliyan 1.26 a watan Fabrairu.

Daga bisani, amfani da data ɗin ya sake ƙaruwa zuwa kusan TB miliyan 1.42 a watan Maris da TB miliyan 1.41 a watan Afrilu, kafin ya kai sabon tarihi na TB miliyan 1.50 a watan Mayu.

MTN, wanda shi ne kamfanin sadarwar wayar hannu mafi girma a Nijeriya, ya samu kusan naira tiriliyan 1.7 daga ayyukan data a rabin farko na shekarar 2026.

Kuɗaɗen shigar kamfanin daga data sun kai naira tiriliyan 1.699 cikin watanni shida, daga naira tiriliyan 1.229 da aka samu a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.

Hakan na wakiltar ƙarin kuɗaɗen shiga da ya kai kusan kashi 38.3 cikin 100.