Duniya

df5b23a3 7122 48d8 b716 714d8bcac07e 1790227360481

Sau takwas sojojin Amurka na yunƙurin kashe kansu a cikin USS Abraham Lincoln, in ji gwamnatin Trump

Gwamnatin Trump ta gasgata halin da jami’an Amurka suka shiga a cikin jirgin ruwan Abraham Lincoln mai dakon jiragen sama, inda ta ce sau takwas jami’an na yunƙurin kashe kansu saboda matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa da yanayin rayuwa a cikin jirgin.

Kwamitin Zaman Lafiya na Duniya zai gabatar da shirin farfado da Gaza na dala biliyan $2.45: Rahoto

Shirin ya ƙunshi tanadin kuɗaɗen samar da matsugunan wucin gadi, kwashe baraguzan gine-gine, gyaran asibitoci, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma tura rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa.

Trump ya yi wa Iran barazana, ya kira ICC ‘marar gaskiya‘, ya sauya sunan AI zuwa ‘SI’

Shugaban Kasar Amurka Trump ya ce a nan kusa za a iya cim ma yarjejeniyar kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Ukraine.

Amurka ta kai ‘yan ci-rani fiye da 25,000 da ta kora zuwa ƙasashen da ba su da alaƙa da su: Bincike

Gwamnatin Trump ta cim ma yarjejeniyoyi da ƙasashe 35 inda ta ware aƙalla dala miliyan 410 don tallafa wa aikin korar.

Afirka

b95da07c ba88 4c98 a026 8da3a7d20cdd 1790426022472

Fiye da mutum 55,000 daga Sudan sun tsere zuwa gabashin Chadi don gudun hijira

Fiye da mutane 400 ne ke tsallakawa ta yankunan kan iyakar Adre da Tine a kowace rana cikin makon da ya gabata, kamar yadda mai kula da harkokin ’yan gudun hijirar yankin na Majalisar Ɗinkin Duniya kan rikicin Sudan ya shaida wa manema labarai.

Wasu karin mayakan RSF sun sauya sheka zuwa Rundunar Sojin Sudan bayan sun gamu da ‘masifu’

Wasu mayaƙa da ke da alaƙa da RSF sun ɓalle tare da shiga Rundunar Sojin Sudan. Kwamandan mayaƙan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan ya ga “masifu” a cikin RSF, tare da yin kira ga sauran mayaƙan ƙungiyar da su ajiye makamansu su koma gida.

Ana samun ƙaruwar Ƙasashen Yamma masu goyon bayan biyan diyyar cinkin bayi: Ghana

A watan Maris, Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da wani ƙuduri da ya ayyana bautar da aka yi ta hanyar safarar bayi waɗanda aka ƙetare Tekun Atlantika da su a matsayin “babban laifin da aka taɓa aikatawa kan bil’adama”.

Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar

Salva Kiir ya ɗauki matakin ne domin kauce wa wani giɓi na tsarin mulki.