Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya

Erdogan ya ce al’ummomi masu ƙarfi da haɗin kai za su iya taimakawa wajen yaƙi da ƙiyayya da tsangwama da kuma nuna wariya ga al’ummar Musulmai.
24 Sep, 2026
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya

Kusan shugabannin ƙasashe 130 ne za su halarci taron, a daidai lokacin da tsarin duniya da aka kafa bayan Yaƙin Duniya na Biyu ke fuskantar barazana, yayin da ita kanta Majalisar Ɗinkin Duniya ke fama da ƙalubale.
20 Sep, 2026
‘Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari’

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya ce akwai yiwuwar Saudiyya na da wasu buƙatun soji sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ’yan Houthi suka kai, kuma Turkiyya za ta duba waɗannan buƙatu ƙarƙashin yarjejeniyar tsaro ta Makkah.
20 Sep, 2026
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata

Hukumomin ruwan Turkiyya sun ce ana zargin jirgin da ya bace mai dauke da mutane 10 ya nutse ne bayan ya kasa amsa kiran da aka yi ta yi masa, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.
2 Sep, 2026

An haƙo wani sassaƙen ɗan’adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya

Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi

Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest

Turkiyya ta ƙaddamar da shirin 2026–2030 na zama cibiyar fasahar AI ta duniya

Trump ya yi ‘murna’ kan yarjejeniyar tsaro ta Makka da Turkiyya da Pakistan da kuma Saudiyya suka yi
14 Aug, 2026
Shugaban Erdogan ya jinjina wa shekara 25 na Jam’iyyar AK kan samar da ‘sauyi mai tarihi’ a Turkiyya
Yayin da jam’iyyar AK ta cika shekaru 25, Erdogan ya ce an kafa ta ne a ranar 14 ga Agustan 2001, da nufin sake fasalin makomar Turkiyya, ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa, da tabbatar da cewa ƙasar za ta iya yanke shawara da kanta.

13 Aug, 2026
Turkiyya ta kama mutum 30 a wani samame da aka kai kan ƙungiyar masu aikata laifuka ta Alihan
A cewar rahoton Hukumar Binciken Laifukan Kuɗi ta Turkiyya (MASAK), yawan hada-hadar kuɗi na kamfanoni da dama da ke da alaƙa da ƙungiyar ya ƙaru sosai bayan shekarar 2020, yayin da aka rarraba wasu kamfanonin tare da canja wurin mallakarsu.

13 Aug, 2026
Turkiyya za ta ci gaba da taka rawa da kuma shiga tsakani a Libya, in ji Ministan Harkokin Waje
Turkiyya tana goyon bayan sulhu tsakanin yankin gabas da na yammacin Libya, a cewar Fidan a yayin da Ankara take ƙarfafa hanyar tattaunawa da zaman lafiya da haɗin a ƙasar.

10 Aug, 2026
Cikin hotuna: Turkiyya ta haskaka muhimman wurare don murnar Yajejeniyar Tsaron Hadin Gwiwa ta Makka
Sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Turkiya, Saudiyya da Pakistan ta zama abubuwan ɗaukar hankali a Ankara da Istanbul, inda aka haskaka muhimman gine-gine don nuna saƙon goyon baya da tsara makoma mai muhimmanci.

3 Aug, 2026
Shugaban sadarwa na Turkiyya ya ce Isra’ila na yi wa yunƙurin zaman lafiya na Gaza zagon ƙasa
Burhanettin Duran ya bayyana ƙudirin Turkiyya na jajircewa wajen tabbatar da halastattun haƙƙoƙin Falasɗinawa.

1 Aug, 2026
Turkiyya ta kama ɗanta’addan FETO da ake nema bisa ƙoƙarin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016
Wanda ake zargin, wani keftin na soji da aka kora kuma tsohon matuƙin helikwafta, ya kasance ana nemansa ruwa-a-jallo a ƙarƙashin wata Jar Sanarwar ta Hukumar ‘Yansandan Duniya.

31 Jul, 2026
Turkiyya ta yi fice a Gasar Duniya ta Rubutu a Kwamfuta da kambi 36
Masu gogayya daga kasashe 34 sun gwada saurin rubutu da rashin kuskure a wajen Gasar Rubutu a Kwamfuta ta Duniya ta Intersteno da ke gudana a Liverpool.

29 Jul, 2026
Turkiyya da Nijeriya sun ƙara ƙarfafa daɗin gwiwa kan ƙera jiragen ruwa
Gwamnatin Nijeriya na son kamfanonin ƙera jiragen ruwa na Turkiyya su zama abokan hulɗa na dindindin wajen haɓaka ƙarfin ƙasar na ƙera jiragen ruwa a cikin gida.

20 Jul, 2026
Turkiyya ta yi kira ga Amurka da Iran su koma kan yarjejeniya, su kuma yi aiki tare da Qatar
Babban jami’in diflomasiyyar Turkiyya ya ce Doha tana amfani da dukkan hanyoyin diflomasiyya don magance rikici tsakanin Amurka da Iran tare da fatan samun ci gaba mai kyau a cikin kwanaki masu zuwa.

18 Jul, 2026
Girgizar ƙasa mai maki 5 ta girgiza gabashin Turkiyya
Girgizar ƙasar ta afka wa gundumar Battalgazi a wani wuri mai zurfi na kilomita 15.59, in ji hukumar bada agajin gaggawa ta Turkiyya.



