Batun kisan shahararren mawakin rap, Tupac Shakur, wanda aka kwashe shekaru da dama ba a warware shi ba, yanzu ya shiga matakin shari’a, yayin da mutumin da ake zargi da hannu a kisan nasa a Las Vegas a shekarar 1996 zai gurfana a gaban kotu.
Duane “Keffe D” Davis, mai shekara 63, na fuskantar tuhuma guda ɗaya ta kisan kai da makami mai hatsari, da nufin inganta, ci gaba ko taimaka wa wata ƙungiyar masu aikata laifuka, dangane da mutuwar Shakur.
Zaɓen alkalan kotun zai fara ne a ranar Litinin, yayin da ake sa ran shari’ar za ta ɗauki kusan wata guda.
Shari’ar za ta sake buɗe ɗaya daga cikin manyan sirrin duniyar hip-hop, wanda ya daɗe yana ɗaukar hankalin jama’a tsawon shekaru. Shakur, wanda aka kuma san shi da sunayen 2Pac da Makaveli, ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin mawakan rap da suka fi yin tasiri a tarihi.
An harbi Shakur a Las Vegas a ranar 7 ga Satumban 1996. Yana cikin wata bakar mota kirar BMW tare da hamshakin mai harkar kiɗa Marion “Suge” Knight, a hanyarsu ta zuwa Club 662, inda Shakur ya shirya yin wasa.
A lokacin da suke tafiya, wata farar mota kirar Cadillac ta zo ta gefensu, sannan aka fara harbe-harbe. Shakur, wanda yake zaune a kujerar gaba ta gefen fasinja, an harbe shi sau da dama. Ya rasu bayan kwanaki shida, yayin da Knight ya tsira.
Batun ya ɗauki tsawon lokaci ba tare da wani ci gaba ba, har zuwa shekarun baya, lokacin da kalaman Davis a bainar jama’a da kuma wani littafin da ya rubuta wanda ya ƙunshi bayanai masu yawa suka sake farfaɗo da binciken.
A lokacin mutuwar Shakur, Davis yana cikin shugabannin ƙungiyar South Side Compton Crips.
An kama Davis a shekarar 2023, kuma ya musanta aikata laifin a gaban kotu.
Ga abin da ya kamata a sani game da shari’ar:
Zaɓen alƙalin kotu zai fara ranar Litinin. Ana sa ran zaɓen alkalan zai ɗauki kwanaki da dama. Bayan haka, masu gabatar da ƙara da lauyoyin da ke kare shi za su gabatar da jawabansu na farko, sannan a fara sauraron shaidun da za su bayyana a gaban kotu.
A cikin kotun, wuraren zama ga jama’a za su kasance kaɗan, kuma za a gudanar da ƙuri’a a kowace rana domin tantance waɗanda za su samu damar shiga kotun.
Za a kuma buɗe wani ɗaki da ke hawa na biyu na kotun ga jama’a, inda za a nuna yadda shari’ar ke gudana kai tsaye.
Wataƙila shari’ar ba za ta bayyana wanda ya harbi Shakur ba
Masu gabatar da ƙara ba sa zargin cewa Davis ne ya yi harbin bindigar a daren da aka kashe Shakur. Saboda haka, mai yiwuwa shari’ar ba za ta tabbatar da wanda ya harbi Shakur kai tsaye ba.
Maimakon haka, masu gabatar da ƙara za su yi ƙoƙarin tabbatar da cewa Davis ne ya bayar da umarnin ko ya ɗauki matakan da suka kai ga mutuwar Shakur, sannan ya samar da bindigar da aka yi amfani da ita wajen harbin mawakin.
Ana sa ran masu gabatar da ƙara za su kira tsakanin shaidu 35 zuwa 45 yayin shari’ar.
















