Cikin ‘yan awanni kaɗan bayan nasarar da Abdul El-Sayed ya samu a zaɓen fid da gwani na takarar Majalisar Dattawa daga Jihar Michigan ta Amurka a ƙarƙashin jam’iyyar Democrat, an samu ƙaruwar rubuce-rubuce da wallafe-wallafe da ke nuna ƙiyayya da ƙyamar Musulmai ta shafukan intanet.
Wani sabon bincike daga Cibiyar Nazari kan Ƙiyayya ta Ƙungiyoyi (CSOH) ya nuna cewa rubuce-rubuce da aka yi kan El-Sayed da cin zarafin Musulunci sun kai aƙalla sau 3,099 a rana ta farko cikin makon da aka ayyana nasararsa, daga aƙalla sau 155 da ake samu a kowace rana cikin watanni biyu da suka gabata kafin zaɓen, adadin da ake ganin ya ƙaru da kashi 1,895 cikin ɗari.
A ranar 5 ga Agusta, ranar da mai hamayya da shi ta amince da shan kaye, saƙonnin ƙiyayya ga Musulunci da aka wallafa game da shi sun kai kusan 7,000 a rana guda.
A wannan makon kaɗai an samu ƙarin rubuce-rubuce da suka nuna ƙyamar Musulunci ƙarara kan El-Sayed, adadin da ya zarce wanda aka samu watanni bakwai da suka wuce.
Sun kai kashi 56.7 cikin 100 na rubuce-rubuce 38,280 da aka yi ta wallafawa na nuna ƙyamar Musulunci game da shi tun daga watan Janairu.
El-Sayed, tsohon jami’in lafiyar jama’a na jihar Michigan wanda ke takarar kujerar Majalisar Dattawan Amurka da Gary Peters ya bari, Musulmi ne. Lamarin ya zama muhimmin abu a cin zarafin da aka yi masa.
Binciken CSOH, wanda ya tattaro rubuce-rubuce daga shafukan X da Facebook da Instagram da YouTube da Reddit da kuma Bluesky, ya gano cewa abubuwan da ake wallafawa sun mayar da hankali ne kan makirci da ke ci gaba da faruwa maimakon ainihin suka ta siyasa.
Manyan sunayen da aka danganta shi da su, sun haɗa da Hamas da Hezbollah tare da rubuce-rubucen da aka yi ta yada wa da ke nuna shi a matsayin “mai jihadi.”
Wasu kuma sun zarge shi da shirin sanya dokar Shari’a, yayin da wani kaso na rubuce-rubucen da aka wallafa ke kira da a mayar da Musulmai da ke ƙasashen Yamma zuwa ƙasarsu ta asali.
An yi ta samun ƙaruwar nuna ƙiyayya
Ba a taƙaita ƙaruwar nuna ƙiyayya ga El-Sayed a rubuce-rubuce da aka wallafa game da shi ba.
A faɗin shafin X kaɗai, CSOH ta bi diddigin rubuce-rubuce 409,640 da ke ƙarfafa ƙyamar Musulunci da shirin makirci a Amurka tsakanin 1 ga watan Yuni zuwa 10 ga Agusta.
Rubuce-rubucen ƙiyayya ga Musulunci da aka wallafa a shafin baki ɗaya sun ninka yawan waɗanda aka tattaro a yini ɗaya na ranar 5 ga Agusta, ranar da aka ayyana nasarar El-Sayed, inda aka samu rubuce-rubuce kusan 12,000.
Adadin da ya ninka sau biyu idan aka kwatanta da wadanda aka samu a cikin kwanaki 30 da suka wuce, inda ya kai 10,000 a rana ta farko.
Bayan kwana shida, masu bincike sun ce, adadin rubuce-rubucen bai ragu ba.
Ƙaruwan yawan ‘yan takara Musulmai
CSOH ya danganta karuwar nuna kiyayyar musulunci ta yanar gizo da wani yunƙurin da aka tsara.
Wanda masu bincike suka ce ya samar da wani mahanga bisa ga ra’ayoyin da aka samo daga ka’idar “Great Replacement”, inda kalaman suka ƙara tsananta a lokuta kamar yaƙin Gabas ta Tsakiya da ƙaruwar adadin ’yan takara Musulmai da ke neman muƙaman gwamnati a Amurka.
Nasarar da El-Sayed ya samu a Michigan na ɗaya daga cikin sakamakon da aka sa ido sosai a kansu a zagayen zaɓen fidda gwani na Amurka na wannan watan, wani ɓangare na shirin zaɓen tsakiyar wa’adi na shekara mai zuwa.
Sai dai abin da ya biyo baya, a cewar masu bincike ya zama tamkar suka ga ɗan takara ɗaya a duk lokacin da wani ɗan siyasa Musulmi ya yi nasara ko ya samu ƙarbuwa.
CSOH ta ce tana sa ran tattara ƙarin sakamakon nuna kyama da kiyayyar Musulmai yayin da ake ci gaba da fafutukar neman zaɓen tsakiyar wa’adi na 2026.
















