Rundunar ’yansandan Jihar Neja da ke arewacin Nijeriya ta tabbatar da gano gawawwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar.
A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, ana zargin ’yanbindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya a kan hanyar.
Kakakin rundunar ’yansandan jihar, Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a Minna a ranar Laraba.
Ya ce bayan samun labarin lamarin a ranar Talata, an tura tawagar ’yansanda da jami’an soji zuwa wurin domin kwashe gawawwakin.
Ya ƙara da cewa an ƙara tsaurara ayyukan bincike da share fagen tsaro a yankin domin tabbatar da cewa babu wata barazana ga tsaro.
Ya ce, “An tura tawagogin ’yansanda da sojoji zuwa wurin da lamarin ya faru; an kwashe gawawwakin, yayin da aka ƙara tsaurara ayyukan share fagen tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.”
Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki kaɗan bayan jami’an tsaro sun ceto mutane 308 da aka sace a hare-hare daban-daban a jihohin Kwara da Neja.
Daga cikin mutanen 308 da aka ceto, 163 an sace su ne daga ƙauyen Woro da ke Ƙaramar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, yayin da wasu 145 aka sace a wani hari na daban a Jihar Neja.
An ceto mutanen ne daga dajin Kainji Lake National Park da ke Ƙaramar Hukumar New Bussa ta Jihar Neja, yayin wani samame na haɗin gwiwa da aka gudanar bisa bayanan sirri.
Aikin ya haɗa da Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa, Rundunar Sojin Nijeriya, Hukumar DSS da Rundunar ’Yansandan Nijeriya.

















