Wani jami’in Iran da ba a bayyana sunansa ba ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Japan, Kyodo News, a ranar Talata cewa Tehran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai, idan Amurka ta ɗauki matakan farko na sassauta matsin lambar soji da take yi wa Iran.
Kamfanin dillanacin labarai na Turkiyya, Anadolu ya ce bai iya tabbatar da sahihancin wannan batu ba da kansa.
Rahoton ya ce tuni aka isar da wannan tayin ga Washington ta hannun masu shiga tsakani.
Jami’in na Iran ya ce tayin ya ƙunshi sake komawa teburin tattaunawa, da nufin cim ma yarjejeniyar da za ta kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin ƙasashen biyu na dindindin.
Sai dai ya yi watsi da yiwuwar ganawa tsakanin Shugaban Iran Masoud Pezeshkian da takwaransa na Amurka Donald Trump a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da ke gudana a New York a wannan makon.
Jami’in ya ce akwai yiwuwar a samu yarjejeniya, amma ya ƙara da cewa Washington dole ne ta nuna “da gaske take kuma ta himmatu” kafin diflomasiyya ta samu ci gaba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin Amurka da Iran, yayin da tattaunawar ƙasashen biyu ta tsaya cak saboda saɓanin ra’ayi kan zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar mashigar ruwa da ake amfani da ita wajen safarar makamashi da kayayyaki.
A ranar 28 ga Fabrairu, Amurka da Isra’ila sun ƙaddamar da yaƙi kan Iran, lamarin da ya sa Tehran ta mayar da martani da hare-hare kan Isra’ila da wasu ƙasashen yankin da ke karɓar kadarorin sojin Amurka.
Bayan ƙasashen biyu sun amince da tsagaita wuta da Pakistan ta shiga tsakani wajen samarwa a watan Afrilu, Amurka da Iran sun rattaba hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad a watan Yuni, wadda ta ba su kwanaki 60 domin tattaunawa kan yarjejeniyar da za ta dawwama.
Sai dai ba da jimawa ba ƙasashen biyu suka koma kai hare-haren ramuwar gayya, yayin da Amurka ta sake kakaba shingen soji kan tashoshin jiragen ruwa na Iran, ita kuma Tehran ta rufe Mashigar Hormuz.

















