Ƙasashen Qatar, Kuwait, Bahrain da Jordan sun yi Allah wadai a ranar Alhamis kan yunƙurin mayakan Houthi na Yemen, waɗanda Iran ke marawa baya, na kai hari yankin Madina na Saudiyya da makami mai linzami mai cin dogon zango, tare da jaddada cikakken goyon bayansu ga Saudiyya.
Ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ta bayyana cewa, rundunar tsaron sararin samaniyarta ta yi nasarar tarewa tare da lalata makamin, sannan ta kuma kakkabo wani jirgi mara matuƙi na mayakan Houthi a Lardin Gabas na ƙasar.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta bayyana yunƙurin a matsayin “babbar tsokana ga Musulmi da kuma rashin kula da rayukan fararen-hula,” tare da cewa hakan ya saɓa wa cikakken ikon ƙasar Saudiyya da dokokin ƙasa da ƙasa.
Ma’aikatar ta sake jaddada cikakken goyon bayan Qatar ga Saudiyya, tare da bayyana goyon bayanta ga dukkan matakan da Saudiyya za ta ɗauka bisa doka domin kare ikonta, tsaronta, yankinta da muradunta.
Ita ma Ma’aikatar Harkokin Wajen Kuwait ta bayyana ƙin amincewarta da ci gaba da kai hare-haren, tana mai cewa hakan babban keta cikakken ikon Saudiyya ne da dokokin ƙasa da ƙasa da kuma dokokin jin ƙai na ƙasa da ƙasa.
Ma’aikatar ta sake jaddada goyon bayan Kuwait ga Saudiyya, da kuma dukkan matakan da masarautar za ta ɗauka domin kare ikonta da tsaronta, tare da kiyaye rayukan ‘yan ƙasa da mazauna ƙasar.
A nata ɓangaren, Ma’aikatar Harkokin Wajen Bahrain ta ce kai hari yankin Madina ba wai barazana ce kawai ga fararen-hula da masu ziyartar Masallacin Annabi ba, har ma da cin zarafi ga martabar wurare masu tsarki na Musulunci, lamarin da ke ɓata wa Musulmi a faɗin duniya rai.
Ma’aikatar ta sake yin kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya ɗauki tsauraran matakai da za su hana aukuwar irin waɗannan hare-hare, domin dakatar da hare-haren Houthi da ake ta maimaitawa, tare da hana kai hari wurare masu tsarki na addini da kadarorin fararen-hula, da kuma hukunta waɗanda suka aikata laifukan da waɗanda ke mara musu baya.
Ƙasar Jordan ma ta shiga cikin ƙasashen da suka yi Allah-wadai da lamarin, inda ta bayyana yunƙurin kai hari yankin Madina da makami mai linzami a matsayin tsokana ga Musulmi, keta cikakken ikon Saudiyya, barazana ga tsaronta da zaman lafiyarta, da kuma keta dokokin ƙasa da ƙasa da yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan ta sake tabbatar da cikakken goyon bayan ƙasar ga Saudiyya, tana mai jaddada goyon bayanta ga dukkan matakan da masarautar za ta ɗauka domin kare tsaro, zaman lafiya, cikakken ikonta da rayukan ‘yan ƙasa da mazauna ƙasar.
A ranar Alhamis ne ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ta sanar da cewa rundunar tsaron sararin samaniyarta ta tare tare da lalata wani makami mai linzami da mayakan Houthi na Yemen suka harba zuwa yankin Madina.
Sai dai mayakan Houthi sun musanta zargin cewa sun yi yunƙurin kai hari Madina.
Yemen na cikin yaƙin basasa tun bayan da mayakan Houthi suka ƙwace babban birnin ƙasar, Sana’a, da wasu yankuna a watan Satumban 2014.
Ƙungiyar haɗin gwiwar ƙasashen Larabawa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya ta fara mara wa gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita baya tun watan Maris na 2015.
Yaƙin dai ya ƙara tsananta a ‘yan makonnin nan, inda mayakan Houthi suka riƙa kai hare-hare akai-akai da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa a cikin ƙasar Saudiyya.

















