Firaministan Spain, Pedro Sánchez, ya karyata rahotannin da ke cewa Amurka ta yi tunanin dakatar da Spain daga NATO saboda sabanin ra’ayi kan rikicin Iran. Rahoton ya danganta da wani sakon cikin gida daga Pentagon wanda ya nuna yiwuwar daukar mataki kan kasashen da ba su goyi bayan matakin soja na Amurka ba.
Spain ta fito a cikin wannan batu ne saboda ta ki amincewa a yi amfani da kasarta ko sararin samaniyarta wajen kai hare-hare kan Iran. Sai dai Sánchez ya jaddada cewa gwamnatin Spain ba ta yarda da bayanan da ba na hukuma ba, yana mai cewa suna dogaro ne da matsayinsu na gwamnati kawai.
Ya kuma tabbatar da cewa Spain na ci gaba da kasancewa mai biyayya ga hadin gwiwa da kawaye, amma cikin iyakar dokokin kasa da kasa. A gefe guda, an ce shawarar ta hada da hanyoyin “hukunta” kasashen da ake ganin ba su bada hadin kai, duk da cewa masana sun nuna cewa NATO ba ta da wata doka kai tsaye da za ta ba da damar dakatar da wata kasa mamba.
Wannan rikici na nuna sabanin ra’ayi da ke ci gaba tsakanin Amurka da wasu kasashen Turai, musamman ganin yadda Donald Trump ya dade yana matsa lamba kan kasashen NATO su kara bada gudummawa da kuma bin manufofin Amurka. Duk da haka, Spain ta ce matsayinta a NATO bai canza ba, kuma batun dakatarwa ba shi da tabbaci a aikace.
MAJIYAR LABARI: AA













