Najeriya Siyasa Tsaro

Shari’ar Yahaya Bello na nan a kotu, na kammala aikina — Shugaban EFCC

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, na nan tana gudana a kotu, yana mai jaddada cewa ya cika alƙawarin da ya ɗauka na gurfanar da shi.

Newstimehub

Newstimehub

12 Jan, 2026

Olukoyede Yahaya 1

Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Nijeriya (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, na nan tana gudana a gaban kotu, yana mai cewa ya kammala duk abin da ya rataya a wuyansa a matsayin shugaban hukumar.

Olukoyede ya faɗi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Channels Television a shirin Sunday Politics, inda ya tunatar da jama’a cewa tun a watan Afrilun 2024 ya sha alwashin yin murabus idan Bello bai fuskanci shari’a ba.

“Akwai shari’o’i uku da muke yi wa Yahaya Bello. Ba ni ne alƙali ba da zan yanke hukunci. Na yi aikina, kuma na cika alƙawarin da na ɗauka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa EFCC ta gudanar da cikakken bincike, ta kuma shigar da ƙara a kotu, inda ya ce al’amari yana ci gaba da samun kulawar shari’a.

Tsohon gwamnan na fuskantar tuhume-tuhume guda 16 da suka shafi zargin damfara da almundahanar kadarori da darajarsu ta kai Naira biliyan 110, tare da wasu mutane biyu — Umar Oricha da Abdulsalami Hudu.

Haka kuma, Bello na fuskantar wata shari’a daban a Babbar Kotun Tarayya, inda ake tuhumarsa da laifuka 19 na almundahanar kuɗi da darajarsu ta kai Naira biliyan 80.2. EFCC ta taɓa ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a watan Afrilun 2024 kan wannan zargi.

Olukoyede ya bayyana cewa ana zargin Bello da fitar da dala $720,000 daga asusun gwamnatin Jihar Kogi zuwa wani bureau de change domin biyan kuɗin makarantar ɗansa tun kafin barin ofis.

“Ana zargin gwamna mai ci da kai tsaye ya fitar da kuɗin gwamnati domin biyan kuɗin makarantar ɗansa gaba ɗaya, a jiha matalauciya kamar Kogi. Wannan abu ne da ba za mu iya yin shiru a kansa ba,” in ji shugaban EFCC.

Majiyar Labari: Channels News