Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da tsarin aika sakamakon zaɓe kai-tsaye ta intanet a cikin ƙudirin gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, bayan muhawara mai zafi tsakanin ta da Majalisar Wakilai.
Yayin da Wakilai suka nemi tsarin ya zama wajibi, Majalisar Dattawa ta dage cewa matakin zai kasance zaɓi ne. A zaman gaggawa da aka yi ranar Talata, majalisar ta yanke shawarar cewa aika sakamakon ta na’ura zai zama matakin farko, amma idan aka samu matsalar intanet, INEC za ta koma amfani da takarda kamar yadda aka saba.
Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin, wanda shugaban majalisar Godswill Akpabio ya amince da shi bayan goyon bayan ƴanmajalisar. Haka kuma, an kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki tare da Majalisar Wakilai. Matakin ya biyo bayan zanga-zangar ƙungiyoyin fararen-hula da jam’iyyun hamayya da suka nuna adawa da rashin wajabta tsarin a baya.
Majiyar Labar: TRT HAUSA














