A ƙoƙarin da ake ci gaba da yi na tabbatar da tsaro da kare rayukan fararen-hula, dakarun sojin Nijeriya a Arewa maso Gabas sun sake samun wata muhimmiyar nasara a yaƙin da ake yi da ‘yan tada ƙayar baya a Jihar Borno.
Dakarun Joint Task Force North East, ƙarƙashin Operation Hadin Kai, sun kama wani da ake zargi da shirin kai harin bam tare da kwace kayan da ake kyautata zaton an tanadar su ne domin kera na’urorin fashewa (IED). An gudanar da wannan samame ne bayan dogon aikin leƙen asiri da aka yi domin tabbatar da tsaron garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama.
A cewar majiyoyin soji, jami’an tsaro da ke bakin aiki a Babban Masallacin Banki sun kama wanda ake zargin, mai suna Abubakar Mustapha, da misalin ƙarfe 5:40 na yammacin Litinin, 29 ga Disamba. An ce an same shi dauke da wasu sassa da ke nuna alamun shirin kai hari.

Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bama ne. A halin yanzu yana tsare a hannun jami’an tsaro domin ci gaba da bincike, musamman don gano masu hannu a lamarin da kuma yiwuwar alaƙarsa da ƙungiyoyin ta’addanci.
A wani lamari mai alaƙa da wannan, sojoji a kan iyakar Nijeriya da Kamaru sun tare wata motar Peugeot da ke ɗauke da buhuna shida na takin urea. Ci gaba da bincike bisa bayanan sirri ya kai ga kama wanda ya kawo kayan tare da ƙwato ƙarin buhuna shida, wanda ya kai adadin da aka kwace zuwa buhuna goma sha biyu.
Rundunar sojin ta bayyana cewa duk waɗanda ake zargi da kayayyakin da aka kwace suna hannun soji, yayin da Operation Hadin Kai ke ci gaba da sintiri da ayyukan tsaro bisa sahihan bayanan sirri domin hana ‘yan ta’adda motsi da kuma kare muhimman gine-gine da fararen-hula.
Sojojin sun kuma buƙaci jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro, suna mai jaddada cewa ƙwarin gwiwar dakarun na nan daram wajen dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabas.














