Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shigar da ƙara a gaban kotu kan tsohon Ministan Shari’a na ƙasa, Abubakar Malami SAN, da ɗansa Abubakar Abdulaziz Malami, bisa tuhume-tuhume 16 da suka shafi almundahanar kuɗi da yawansu ya kai Naira biliyan 1.014.
Bayan Malami da ɗansa, wata mata mai suna Hajia Bashir Asabe na daga cikin waɗanda ake tuhuma a shari’ar. Gwamnati na zargin su da haɗa baki wajen satar kuɗaɗe da ɓoye su, kuɗaɗen da ake cewa an gano su a wani bankin kasuwanci.
A cewar takardun tuhuma, tsakanin watan Yulin 2022 zuwa Yunin 2025, waɗanda ake zargin sun sayi Kamfanin Metropolitan Auto Tech Limited domin amfani da shi wajen ɓoye asalin inda kuɗaɗen suka fito da kuma yadda ake motsa su daga wuri zuwa wuri.
Gwamnati ta bayyana cewa wannan aiki ya zama almundahanar kuɗi a ƙarƙashin dokokin Nijeriya, wanda ya saɓa wa Sashe na 21(c) na Dokar Hana Satar Kuɗi ta 2022, tare da hukunci a ƙarƙashin Sashe na 18(3) na dokar.
Abubakar Malami ya riƙe muƙamin Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a daga 2015 zuwa 2023 a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.














