Aƙalla mutum uku, ciki har da mataimakin shugaban wata makarantar sakandare, sun rasa rayukansu bayan wasu ’yanta’adda dauke da muggan makamai sun kai hari kan wata al’umma da makaranta a Jihar Kogi da ke tsakiyar Nijeriya ranar Laraba.
A cewar rundunar ’yansanda, maharan sun kutsa cikin al’ummar Iluke Bunu ne a kan kusan babura 40, inda suka jefa mazauna yankin da ɗalibai cikin firgici yayin da suka kaddamar da harin.
Lamarin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da ke addabar sassa da dama na Nijeriya, inda al’ummomi da cibiyoyin ilimi ke ci gaba da fuskantar barazana daga masu aikata laifuka.
Jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da masu aikin sintirin sa-kai sun garzaya wurin tare da fafatawa da maharan.
Bayan musayar wuta mai zafi, ’yanta’addan sun tsere zuwa cikin dazukan da ke kusa da yankin.
Rundunar ’yansanda ta ce an kashe wani da ake zargin ɗanta’adda ne a yayin musayar wutar, yayin da jami’an tsaro suka ƙaddamar da farautar sauran waɗanda suka tsere.
Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai mataimakin shugaban makarantar sakandaren da aka kai wa harin, wani dattijo mai shekaru 70 da kuma wani yaro ɗan shekara shida.
Haka kuma, an tabbatar da cewa wani jami’in tsaro ya samu raunuka yayin aikin.
Duk da cewa an fara samun fargabar cewa an yi garkuwa da wasu ɗalibai a lokacin harin, rundunar ’yansanda ta ce har yanzu babu cikakkiyar shaida da ke nuna cewa an yi garkuwa da ɗalibai da yawa. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa makarantu a Nijeriya.
Har yanzu akwai ɗalibai da dama da aka yi garkuwa da su daga Jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya a watan da ya gabata, waɗanda ba a san inda suke ba.
Hukumomi sun ce suna ci gaba da ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya a yankin da abin ya shafa tare da tabbatar da cewa an kamo tare da hukunta waɗanda suka aikata harin.

















