Gabas Ta Tsakiya

Shugaba Trump ya jingina faɗaɗa harin soji kan Iran don ƙarancin makaman tsaron samaniya — rahoto

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan damuwa game da ƙarancin tarin makamai masu linzamin Amurka da taɓarɓarewar lammura a yankin da kuma barazana ga ƙwayenta yankin Gulf.

Newstimehub

Newstimehub

26 Jul, 2026

3fe07c00 ff1d 4151 8dc2 b4970b65635b 1776045002213

Shugaba Donald Trump ya dakatar da shirin tsananta matakan soji kan Iran cikin gaggawa bisa ƙarancin tarin makamai masu linzami na tsaron sararin samaniyar Amurka, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito.

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan wata tattaunawa ranar Jumma’a da shugabna ya yi da manyan masu ba da shawara da jami’an majalisar zartarwa.

Rahotanni sun ce jami’an soji sun yi gargaɗin cewa sabunta gagarumin yaƙi zai iya ƙarasa makamai masu linzami na tsaron sararin samaniya samfurin Patriot da sauran makamai na tsaron sararin samaniya da ake bukata wajen kare dakarun Amurka da sansanonin sojinta a Gabas Ta Tsakiya.

Rahoton ya ce gwamnatin Shugaba Trump ta kuma damu game da yadda ƙara yawan hare-hare kan Iran zai iya janyo ramuwar gayya mai ƙarfi daga Iran tare da nesanta ƙawayen yankin Gulf daga Amurka da kuma tsananta matsalolin makamashi da na gudun hijira.

Ƙalubalen diflomasiyya

Rahotanni sun ce Janar Dan Caine, shugaban majalisar manyan hafsoshin Amurka, ya yi gargaɗi a ɓoye cewa sake fara babban yaƙi zai yiwu, amma zai rage adadin makamai masu linzami na kakkaɓo makamai da hedikwatar tsaron Amurka, wadda ke jagorantar ayyukan soji a Gabas Ta Tsakiya, ke da su.

Daraktan watsa labaran fadar White House Steven Cheung ya ce Trump “ya kasance a ko wane lokaci yana cewa shi ya fi son mafita ta diflomasiyya, amma ya ci gaba da riƙe dukkan zaɓi idan Iran ta ci gaba da ayyuka na ta’addanci a Mashigar Hormuz ko kuma a kan ƙawaye.”

Cheung ya ƙara da cewa “za ta kasance hikima mai kyau ga Iran idan ta yi aiki domin cim ma wata yarjejeniya, idan ba su yi hakan ba, sun san abin da zai faru.”

Rahoton ya ce Trump ya kasance yana tunanin yadda zai ci gaba a rikici da Iran da kuma yadda za a sake buɗe Mashigar Hormuz yayin da farashin mai ke tashi biyo bayan sabunta yaƙi.

Jaridar ta ce diflomasiyya ta katse kuma hare-haren da Amurka ta kai kwanan nan bisa ga alamu ba su yi tasirin rage ƙarfin halin Iran ba.

Ta kuma ba da rahoton cewa wasu manyan jami’an Amurka suna shakkar cewa sabunta manyan hare-hare za su iya matsa wa Tehran ta koma kan teburin tattaunawa, suna masu cewa ƙarin hare-hare za su iya ƙarfafa haɗin kai na cikin gida ga shugabancin Iran.