Nijeriya

Ana fargabar ɗalibai sun maƙale bayan da gini mai ɗakuna 90 ya rufta da su

Hukumomin sun ce ba san adadin waɗanda suka mutu ba kuma ba za a iya tantance waɗanda suka maƙale ba, yayin da ake aikin ceto.

Newstimehub

Newstimehub

27 Jul, 2026

e702123e de92 4bd2 8545 daded88afa7f 1785156014370

Wani bene mai hawa uku inda ɗalibai na kwalejin kimiyya d fasaha na Tarayya ta Oko ya rufta a Amokpala, da ke Oko, a ƙaramar hukumar Orumba Ta Arewa a jihar Anambra kudu maso gabashin Nijeriya, inda ɓaraguzai suka danne ɗaliban da ba a san adadinsu.

Ginin, wanda aka bayyana da suna Elite Five Star Lodge, ya rufta ne ranar Lahadi da dare, in ji rahotanni.

Ruftawar gidan kwanan ɗaliban ya tayar da hankalin mazauna wurin da ɗalibai yayin da ake ta jin kukan neman ɗauki daga ƙarƙashin ɓaraguzai.

Masu ba da taimakon gaggawa sun ƙaddamar da ayyukan ceto, inda jami’ai daga daga rundunar ‘yansandan jihar Anambara da hukumar ‘yan kwana-kwanan jihar da ma hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar da sauran jami’an tsaro suka hallara a wurin.

Kawo yanzu dai an fitar da wasu da suka ji rauni a ruftawar benen kuma an garzaya da su wani asibiti a Oko domin samun magani.

Sai dai kuma masu aikin ceto na ci gaba da aikin neman waɗanda aka yi imanin cewa suna maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan.

Hukumomi sun ce ba a san asalin adadin waɗanda suka mutu ba kuma ba za a iya bayyana adadin waɗanda suka maƙale ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Anambara, SP Tochukwu Ikenga ya ce wata tawagar jami’an tsaro a ƙarƙashin jagorancin ‘yansanda ta tsare wurin da sauri inda ta yi ta jagorantar aikin ba da agajin gaggawa domin tsare rayuka.

Ya yi kira ga mazauna garin su kwantar da hankulansu da kuma guje wa yaɗa labaran da ba ba su da tushe tare da ƙaurace wa wurin da lamarin ya faru domin bai wa ma’aikatan ba da agaji damar yin aikinsu.

Ya ƙara da cewa rundunar ‘yansandan jihar za ta ba da ƙarin bayanai duk lokacin da aka samu sahihan bayanai.