Rundunar ’yansandan Nijeriya ta ce ta kama mutane 262 da ake zargi da aikata munanan laifuka, tare da kuɓutar da mutane 27 da aka yi garkuwa da su, a ayyukan da ta gudanar a faɗin ƙasar tsakanin ranar 5 zuwa 11 ga watan Satumba nan.
Rundunar ta kuma ce ta kwato bindigogi 34 da harsasai 375 da kuma motoci 11. An kuma kashe wasu ’yanbindiga 11 a yayin samamen.
Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa wadda CSP Aniete Iniedu ya fitar kan nasarorin da aka samu a fannin ayyukan rundunar ‘yansandan Nijeriya karkashin jagorancin Sufeto-Janar na ‘Yansanda, IGP Olatunji Rilwan Disu.
Kazalika Iniedu ya ce an kama waɗanda ake zargin da laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane da fashi da makami da kisan kai, da kuma zarginsu da zama ’yanbindiga da ‘yan ƙungiyoyin asiri da masu safarar mutane da safarar miyagun ƙwayoyi da kuma waɗanda ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati.
Rundunar ta ce an samu rahotannin kisan kai 50 da fashi da makami 28 da garkuwa da mutane 27 da kuma hare-haren ’yanbindiga 22 a tsakanin wadannan ranakun.
A Jihar Delta, ’yansanda sun kuɓutar da wani mutum mai shekaru 60 da aka yi garkuwa da shi, bayan musayar wuta da waɗanda suka sace shi.
A jihar Sokoto, an kashe wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yanbindiga ne yayin wani samame da aka kai domin dakile wani shirin kai hari, an kwato bindigar AK-47 da harsasai 28.
A Jihar Kaduna kuwa, jami’an tsaro tare da ’yan sa-kai da mafarauta sun kai samame sansanonin ’yanbindiga, inda aka kuɓutar da mutane biyu da aka yi garkuwa da su, sannan aka kashe mutane biyu da ake zargin ’yanbindiga ne.
Sai dai ’yansanda sun ce mafarauta uku sun rasa rayukansu, yayin da wani ya samu raunin harbin bindiga.
Sai kuma Jihar Akwa Ibom, inda jami’an tsaro suka dakile wani shirin garkuwa da mutane, kana suka kwato wata bindiga da harsasai da kwale-kwale guda biyu.
Rundunar ’yansandan ta ce ana ci gaba da bincike da kuma kokarin kama sauran waɗanda ake zargi.

















