Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan ‘yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu

Nijeriya ta nuna matukar damuwa kan yadda lamarin ya faru a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-haren ƙyamar baƙi da kuma ƙyamar sauran ’yan Afirka a Afirka ta Kudu.

Newstimehub

Newstimehub

12 Sep, 2026

27279882 7681 4cec bd22 8a73de62af82 1789208851340

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi kakkausar suka dangane da kisan wasu ’yan Nijeriya biyu da aka yi kwanan nan a Afirka ta Kudu, tare da yin kira da a gudanar da bincike cikin gaggawa da gaskiya kan yanayin da ya jawo mutuwarsu.

Waɗanda abin ya shafa su ne Bishop Taiwo Michael Fakunle, wanda rahotanni suka ce an kashe shi a gidansa da ke Kensington, Johannesburg, a ranar 4 ga Satumban 2026, da kuma James Uchechukwu Nwankwo, wanda ya rasu a ranar 5 ga Satumba bayan wani bincike da jami’an Hukumar ’Yansandan Afirka ta Kudu suka gudanar a Somerset da ke Cape Town, wanda ake zargin ya yi tsauri.

Nijeriya ta nuna matukar damuwa kan yadda lamarin ya faru a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-haren ƙyamar baƙi da kuma ƙyamar sauran ’yan Afirka a Afirka ta Kudu. Gwamnatin ta ce kashe-kashen na haifar da tambayoyi masu muhimmanci game da tsaron ’yan Nijeriya da sauran ’yan ƙasashen waje a kasar.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci hukumomin Afirka ta Kudu da su gudanar da cikakken bincike kan lamuran guda biyu tare da tabbatar da cewa duk wanda aka samu da hannu a ciki ya fuskanci hukuncin doka. Ta kuma bayyana damuwa ta musamman kan zargin da ya shafi jami’an ’yansanda a mutuwar Nwankwo.

Nijeriya ta kuma tunatar da cewa ta daɗe tana kokarin warware matsalar ƙyamar baƙi da ƙyamar ’yan Afirka tare da Afirka ta Kudu ta hanyar diflomasiyya, ciki har da Yarjejeniyar Fahimtar Juna kan kafa tsarin gargaɗin farko (Early Warning Mechanism), wadda Nijeriya ta ce ta rattaɓa hannu a kanta yayin da take jiran sanya hannu daga ɓangaren Afirka ta Kudu.

Gwamnatin ta ce tana duba yiwuwar daukar wasu ƙarin matakai domin samun hadin kan Afirka ta Kudu wajen magance matsalar hare-haren da ake kai wa ’yan Nijeriya da sauran ’yan Afirka.

Nijeriya ta mika saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, abokansu da al’ummar Nijeriya da ke Afirka ta Kudu, tare da addu’ar Allah Ya ji kan mamatan kuma Ya ba iyalansu haƙurin jure wannan rashi.

Ko a wannan makon sai da Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da dukkan ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da umartar ’yan majalisa, kwamitoci, jami’ai da ma’aikata da su ƙaurace wa ayyukan majalisa da hukumomin Afirka ta Kudu suka shirya ko suka karɓi baƙuncinsu.