Sojoji na Operation Hadin Kai sun hana harin bam na Boko Haram a Gwoza, Jihar Borno, inda suka kashe masu harin bam uku da wasu makiyan da ke tare da su a Guduf–Pulka. Bayan samun bayanan sirri, sojoji tare da matasa masu sa kai sun dakile masu hari kafin su isa wuraren jama’a.
An kwato kayan harbi ciki har da bamu da kayan fashewa (IED), bindigogi AK-47 guda hudu, sannan an lalata babura biyu da ake amfani da su wajen kai harin. Masu hari na daga rukunin JAS na Ali Ngulde dake tsaunukan Mandara.
Hukumomi sun ƙara himma wajen gano da dakile hare-hare tare da hadin kai da matasa a unguwanni. Ana roƙon mutane su rika bayar da rahoton duk wani mutum ko motsi da ya zama abin zargi. Hare-haren baya-bayan nan sun nuna barazanar tsaro a Borno da Yobe.














