Kungiyoyin ƙwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da Trade Union Congress (TUC) sun umarci dukkan ma’aikatan da ke ƙarƙashin albashin Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) da su koma aiki nan take. Umarnin ya biyo bayan doguwar tattaunawar sulhu da aka yi da Ministan FCT, Nyesom Wike, inda aka cimma matsaya kan korafe-korafen da suka haddasa yajin aikin.
A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da TUC da NLC suka fitar, ƙungiyoyin sun ce an warware dukkan ƙorafe-ƙorafen da Joint Union Action Committee (JUAC) ta gabatar, tare da tabbacin cewa ba za a gallaza wa kowane ma’aikaci ba saboda shiga yajin aikin. Haka kuma, an amince da janye dukkan shari’o’in da suka shafi rikicin a National Industrial Court (NIC).
Kungiyoyin sun bayyana cewa tattaunawar ta samu nasara ne da shiga tsakani na shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan FCT, Mohammed Bomoi, inda Ministan ya yi alkawarin girmamawa da ci gaba da tattaunawa domin kyakkyawar alaka a wurin aiki. An kuma bukaci dukkan mambobi su bi umarnin komawa aiki domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a masana’antu.
Yajin aikin ya haddasa tsaikon ayyuka a sassa da hukumomin FCTA da FCDA tun daga 19 ga Janairu, sakamakon korafe-korafe kan rashin tura kudaden fansho da NHF, jinkirin biyan alawus-alawus na karin matsayi da sauran batutuwa. Bayan umarnin kotu na dakatar da yajin aikin da kuma gargadin tsaro, komawar ma’aikata na nuni da dawowar ayyuka a babban birnin ƙasa.














