Hukumar da ke kula da sarrafa makamai a Najeriya ta ce a ranar Alhamis ta lalata makamai 2,819 marasa izini, tsofaffi da kuma wadanda suka daina aiki, a yunkurin rage rashin tsaro da yawaitar makamai ba bisa ƙa’ida ba ke haddasawa.
Shugaban hukumar, Johnson Kokumo, ya ce an lalata makaman har abada kuma ba za a iya farfaɗo da su ba a wani aikin lalata su a bainar jama’a da aka shirya domin hana sake damar amfani da su.
An lalata makaman ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fama da ‘yan bindiga, satar mutane, ta’addanci, da rikice-rikicen al’umma—abubuwan da hukumomi ke cewa suna ci gaba ne ta yaduwar makamai marasa izini.
Jami’ai sun ce tun bayan kafuwar hukumar a 2021 an ƙwace fiye da makamai 21,000 marasa izini, kuma an riga an lalata fiye da 19,000 don tabbatar da cewa an cire su daga zagayowar makamai gaba ɗaya.

















