Dakarun rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da ta’addanci a arewa maso gabashin Nijeriya sun yi nasarar daƙile yunƙurin sace mutum 31 da ‘yan ta’adda suka yi a jihar Borno.
Wata sanarwar da muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar Operation Hadin Kai, Keftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Jumma’a ce ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar daƙile yunƙurin sace mutanen ne a kan hanyar Buratai zuwa Kamuya a ƙaramar hukumar Biu ta jihar Borno.
“Da misalin ƙarfe 3:45 na ranar 31 ga watan Yuli na shekarar 2026, dakarun bataliya ta musamman da ke Dutsen Kura sun gano ‘yanta’addan Boko Haram/ISWAP ta hanyar tsarin tattara bayanan sirri kai-tsaye yayin da suka tare motocin fararen hula huɗu kuma suka sace waɗanda ke cikinsu,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa nan take ne bataliyar ta tura wasu dakarun ko-ta-kwana su bi ‘yanta’addan da suka tsere ta yankin Mangari–Dora.
“Dakarun sun yi kiciɓis da masu tayar da ƙayar bayan kuma sun buɗe musu wuta, lamarin da ya tilasta musu su yi watsi da fararen hulan da suka sace da kuma motocin fararen hula hudu ɗin kafin su tsere zuwa cikin dazukan da ke kusa a cikin ruɗani,” in ji rundunar.
Ta ƙara da cewa baya ga dukkan fararen hulan 31 da suka kuɓutar yayin samamen, dakarun sun ƙwato baburan da ‘yanta’addan da ke tserewa suka bari a baya.
Daga baya sojojin sun raka fararen hulan da suka ceto garin Buratai inda suka ci gaba da tafiyarsu cikin aminci
A wani labari mai kama da hakan, dakarun rundunar Operation Wabaizigan sun kuɓutar da mutum 14 da aka yi garkuwa da su a jihar Edo.
Wata sanarwar da mataimakin daraktan watsa labarai na rundunar a birged na 4 na sojin Nijeriya, Keftin Kennedy Anyanwu, ya fitar ranar Jumma’a a Benin City ta ce da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar Alhamis ne dakarun suka sami labarin garkuwa da mutane kan babbar hanyar Benin zuwa Legas a ƙaramar hukumar Ovia ta jihar Edo.
Samun labarin garkuwa da mutanen ke da wuya sai dakarun suka bi masu garkuwa da mutanen inda suka matsa musu, lamarin da ya tilasta wa masu aika-aikar sake 11 daga cikin waɗanda suka kama kuma suka tsere zuwa dazukan da ke kusa.
A wani samame na bibiyar lamarin da dakarun suka kai washe gari ranar Jumma’a, sun bincika lungu da saƙo na dajin kuma sun yi nasarar ceto sauran mutane ukun, lamarin da ya mayar da adadin waɗanda aka kuɓutar ɗin 14, in ji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa binciken lafiyar waɗanda aka ceton ya tabbatar da cewa mutanen suna lafiya, tana mai ƙarawa da cewa ana kan ƙoƙarin kama masu garkuwa da mutanen da suke tserewa.

















