Aƙalla mutane 13 ne aka kashe, yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu hare-hare daban-daban da aka kai kan al’ummomi a ƙananan hukumomin Jos ta Kudu, Mangu da Riyom na Jihar Filato.
Hare-haren sun faru ne a daren Lahadi, inda aka kashe fasinjoji tara da ke tafiya zuwa Jos bayan wasu da ake zargin ’yanta’adda ne sun buɗe wa motarsu wuta a al’ummar Dungus da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
Mai magana da yawun ƙungiyar Berom Youth Moulders (BYM), Rwang Tengwong, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 9:40 na dare, lokacin da aka kai wa motar harin, kamar yadda tashar Channels Television ta Nijeriya ta ruwaito.
Tengwong ya ce waɗanda abin ya rutsa da su fasinjoji ne da ke tafiya zuwa Jos lokacin da maharan suka buɗe wa motarsu wuta. Ya ƙara da cewa an garzaya da wasu daga cikin waɗanda suka jikkata zuwa asibitoci, inda daga bisani wasu daga cikinsu suka mutu.
Ya ce ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe mamba ne na Operation Rainbow, yana bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
A wani hari na daban a ƙaramar hukumar Mangu, wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai hari kan al’ummar Vodni da ke gundumar Pushit cikin dare, inda suka kashe mutane biyu.
Wasu mutane huɗu kuma sun samu raunukan harbin bindiga, kuma ana kula da su a wani asibiti da ke garin Mangu.
Haka kuma, a Ƙaramar Hukumar Riyom, an kashe wasu mutane biyu a wani hari na daban da aka kai a Tahoos kusan a lokaci guda.
Sabbin hare-haren sun sake haifar da damuwa kan matsalar tsaro a wasu sassan Jihar Filato, yayin da mazauna yankunan da al’ummomi ke ci gaba da yin kira da a ɗauki ƙarin matakan kare rayuka da dukiyoyi.
Da aka tuntubi Kwamishinan ’Yansandan Jihar Filato ta waya, Ayo Faniyan, ya tabbatar da cewa an kai hare-haren, amma ya ce rundunar tana ci gaba da tattara bayanai kan abubuwan da suka faru.
Ya ƙara da cewa rundunar ’yansanda za ta fitar da sanarwar a hukumance bayan ta samu cikakkun bayanai game da hare-haren.

















