Hukumar ’yan sandan Jihar Kaduna ta karyata jita-jitar da ta bazu a kafafen watsa labarai da ke cewa an yi garkuwa da masu ibada fiye da 100 a wani coci da ke ƙauyen Kurmin Wali, inda ta bayyana cewa babu wata hujja ko sahihan bayanai da ke nuna cewa irin wannan mummunan hari ya faru.
Kwamishinan ’yan sandan jihar ya kalubalanci masu yaɗa labarin da su kawo sunayen waɗanda ake zargin an yi garkuwa da su, yana mai cewa ana ƙoƙarin tayar da hankalin jama’a da karya zaman lafiyar da aka samu.
Shugaban Karamar Hukumar Kajuru, Dauda Madaki, ya ce ya tura jami’an tsaro zuwa cocin da aka ambata, amma ba su tarar da wata alama ta kai hari ba, inda dagacin ƙauyen da shugaban matasa ma suka tabbatar da cewa babu wani abu makamancin haka da ya faru. Haka nan Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da shugabannin CAN sun ce bayanan garkuwar ƙarya ne tsagwaronta.














