A gaskiya wannan wani muhimmin mataki ne a tattalin arzikin Najeriya, domin fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a goge bashin da kamfanin man fetur na ƙasa NNPC Ltd ke bin gwamnati na kusan $1.42bn da kuma Naira tiriliyan 5.57.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin tsaftace bayanan kudi na NNPC tare da karfafa gaskiya da bayyananniyar ma’amala a bangaren man fetur.
Rahoton ya nuna cewa an amince da wannan a taron asusun tarayya bayan wani kwamiti ya bada shawarar daidaita alakar kudi tsakanin NNPC da gwamnati. Gogewar bashin ta ƙunshi nau’ukan wajibai daban-daban har zuwa ƙarshen 2024, ciki har da yarjejeniyoyin rabon mai, nauyin samar da mai a cikin gida, da kuma kudaden haya da haɗin gwiwa da kamfanonin mai.
Sai dai gwamnati ta ce har yanzu tana bin wasu kudaden daga Janairu zuwa Oktoban 2025, tare da rikicin tsohon bashi na dala $42.37bn daga shekarar 2011–2017 wanda bai kammalu ba. Wannan mataki na daga cikin shirin Tinubu na tabbatar da gaskiya a harkokin man fetur, musamman yayin da ake shirin sayar da hannun jarin wasu gidajen mai da iskar gas na ƙasa.
Majiyar Labari: Reuters














