Sakataren Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci Najeriya ta kara taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar kasashen Afirka a kokarin sake duba da kuma gyara tsarin tafiyar da al’amuran duniya.
A wata ganawa da ya yi da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a gefen taron African Union da aka gudanar a Addis Ababa, Guterres ya nuna cewa Najeriya na da karfi, yawan jama’a da kuma tasirin da zai ba ta damar zama abin koyi a nahiyar. Ya kara da cewa irin rawar da Najeriya ke takawa a harkokin tsaro, tattalin arziki da diplomasiyya na iya taimakawa wajen tura Afirka gaba a wannan sabon salo na sauye-sauyen duniya.
Guterres ya kuma nuna cikakken goyon baya ga bukatar Najeriya ta samun kujerar dindindin a Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (UN Security Council). Ya ce yawan al’ummar Najeriya, tsarin dimokuradiyyarta, da yalwar albarkatun kasa da na dan Adam sun sanya ta cikin kasashen da za su iya wakiltar Afirka a matakin duniya.
Haka zalika, shugaban na MDD ya yabawa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Bola Tinubu ke aiwatarwa, tare da jinjina wa rawar da Najeriya ke takawa wajen inganta zaman lafiya a yankunan Sahel da ECOWAS, duk da kalubalen tsaro da take fuskanta a gida.
A nasa bangaren, Shettima ya gode da goyon bayan MDD, yana mai jaddada kudurin Najeriya na ci gaba da aiki tare da kasashen duniya. Ya kuma sake kira da a yi gyaran fuska ga Majalisar Dinkin Duniya domin tsarin ya dace da yanayin duniya na yau, tare da karfafa wakilcin Afirka.














