Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, ya nuna damuwa kan wani sabon mataki da hukumar EFCC ta dauka domin karɓe gidansa da ke Maitama a Abuja.
Ya ce jami’an hukumar sun isa gidansa da safiyar Talata domin aiwatar da umarnin kotu na kwace kadarorin, lamarin da ya zo bayan wasu hare-hare da aka kai a baya kan wasu kadarorinsa a Babban Birnin Tarayya.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC na aiwatar da wannan aiki ne bisa sahihin umarnin kotu karkashin dokar hukumar, wanda ke ba ta ikon bincike da kuma kwato kadarorin da ake zargin sun samo asali daga haramtattun ayyuka.
A kwanakin baya, jami’ai sun shiga wasu gidaje da ofisoshin Malami suna sanya alamar kwace su, abin da ya kara tayar da ce-ce-ku-ce.
Sai dai Malami ya amince cewa akwai umarnin kotu tun ranar 6 ga Janairu 2026 na kwace kadarorin nasa, amma ya ce an ba shi kwanaki 14 ya mayar da martani kuma ya riga ya yi hakan ta hanyar shigar da kara domin a soke umarnin. Ya kuma zargi jami’an EFCC da tsoratar da iyalinsa yayin aikin, yana mai cewa sun shiga gidaje da yawa cikin yanayi mai tsauri.
Malami ya kuma yi zargin cewa matakin da ake dauka yana da alaka da siyasa, yana mai cewa akwai alamun tsangwama saboda burinsa na tsayawa takarar gwamna. Duk da haka, EFCC ta jaddada cewa dukkan matakan da take dauka suna bisa doka ne kuma karkashin ikon kotu.














