Kamfanin Wutar Lantarki na Ghana (ECG) ya sanar cewa za a fuskanci katsewar wutar lantarki a yankunan Tsakiya da Gabas da Yammacin ƙasar a ranar Alhamis, 13 ga Agustan 2026.
Katsewar wutar na daga cikin wani ɓangare na ayyukan gyara da kamfanin ya tsara da nufin ƙara ingancin wutar lantarki.
Kazalika ECG ya ce al’ummomin da abin ya shafa za su fuskanci katsewar wutar lantarki ta tsawon awanni huɗu zuwa bakwai, ya danganta da wurin da suke.
Yankin Tsakiya
An tsara gyaran ya kwashe tsawon awanni bakwai a Yankin Tsakiya, tun daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 4:00 na yamma, kamar yadda sanarwar ECG ta bayyana.
Wuraren da abin zai shafa sun hada da garin Amurka da Sabon Kasuwa da Colomba da Akweley da Ofaako da Papaase da Jei Krodua da Adawukwa da garin Bawjiase da kuma al’ummomin da ke kewaye da su.
Yankin Gabas
Kazalika a Yankin Gabashin ƙasar, wani rukuni na al’ummomi za su fuskanci katsewar wutar lantarki daga karfe 9:00 na safe zuwa karfe 1:00 na rana.
Sun haɗa da yankunan Saarfi da Ahantang da Ampayoo da Ataaso da Owusukrom da Apradang da Yawkorkor da Akroma Gold da Oworobrs da Insuta Everyday da Adensua Mission da Isaac Hotel da Abenase da Bandoh da Abusco da kuma Akutuase.
Wuri na biyu a yankin da zai fuskanci katsewar wutar lantarki daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 2:00 na rana, sun haɗa da Amanase da Mankrong da Asuboi da Kyekyewere da kuma Ayeeh Apeatu.
Yankin Yamma
A Yankin Yamma, an tsara soma gyaran daga ƙarfe 9:00 na safe zuwa 3:00 na yamma.
Al’ummomin da abin ya shafa sun haɗa da Amobaka da Diaso da Modaso da Ankwaso Juabo da Wassa Ayiem da Sraha da Agona Port da Ntom da New Obuasi da Nyinawusu da Some Asamang da Akwaboso da Subin da Ameyaw tare da yankunan da ke kewaye.
ECG ya ce za a yi aikin ne don ƙarfafa hanyar sadarwa ta wutar lantarki da inganta ayyukan kamfanin.
Kamfanin ya nemi afuwa game da wannan tsaiko da za a fuskanta, sannan ya yi kira ga abokan cinikayyarsa da abin ya shafa da su sa ido kan lokutan da aka tsara na yin gyare-gyaren.

















