Dakarun tsaron Nijar sun sanar da kashe ’yan ta’adda 17 a jerin samame da aka gudanar tsakanin 16 zuwa 22 ga Fabrairu 2026. Rahoton ya fito ne daga cibiyar haɗa kan ayyukan jami’an tsaro ta ƙasar (CICO), kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ruwaito.
A cewar rahoton, jami’an tsaro sun kuma kama mutane 33 da ake zargi da aikata laifuka ko taimaka wa masu laifi, inda aka miƙa su ga hukumomin da suka dace. Hakan na daga cikin matakan da ƙasar ke ɗauka na ƙarfafa yaƙi da ta’addanci da safarar haramtattun kaya.
Jami’an sun ƙwace nakiya 1,098, kilogram 48 na tabar wiwi, da lita 23,250 na man fetur da aka shigo da shi ba bisa ƙa’ida ba, tare da daruruwan miyagun ƙwayoyi. Hukumomi sun ce ƙwacewar na nuna ci gaba a ƙoƙarin dakile laifukan kan iyaka.
Rahoton ya kuma ambaci faruwar al’amuran da suka shafi abubuwan fashewa sau uku cikin watan. Masana sun yi nasarar warware biyu, yayin da na uku ya fashe ba tare da jawo asarar rai ba.














