A daren Talata, dorinar ruwa da suka fito daga wani kogi a ƙauyen Hinna, ƙaramar hukumar Yamaltu/Deba a Jihar Gombe, sun mamaye gonaki da dama inda suka lalata amfanin gona da manoma ke shirin girba, lamarin da ya jefa su cikin baƙin ciki da fargabar rasa abin dogaro.
An kiyasta cewa gonaki 17, masu fadin kusan hekta 14, sun lalace baki ɗaya, tare da asarar kuɗi da ta kai kimanin naira miliyan bakwai, abin da ke barazana ga rayuwar manoman da kuma tsaron abinci a yankin.














