An saki alƙalin jihar Kebbi da aka yi garkuwa da shi, Faruku Bunza, in ji rundunar ‘yansandan jihar.
An sace Bunza ne ranar 26 ga watan Yuli a gidansa da ke kan hanyar Zogirma a Ƙaramar Hukumar Bunza ta jihar Kebbi.
An yi garkuwa da alƙalin ne jim kaɗan bayan ya dawo daga Sokoto.
Da yake tabbatar da lamarin ranar Litini, mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, Bashir Usman, ya ce iyalin alƙalin da Ma’aikatar Sharia’ar jihar ne suka tabbatar da cewa an saki Bunza.
Usman ya ce masu garkuwa da mutanen sun nemi kudin fansa, yana mai ƙarawa da cewa rundunar ‘yansandan jihar Kebbi ta tabbatar da matsayarta ta ƙin biyan kudin fansa.
Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kebbi bai bayyana ba ko an biya kudin fansa kafin a saki alƙalin ko ba a biya ba.
“Rundunanar ‘yansandan jihar Kebbi tana son ta tabbatar wa jama’a cewa an saki Mai Shari’a Faruk Hassan Bunza, wani alƙali na babban kotun jihar Kebbi wanda aka sace daga gidansa a Ƙaramar hukumar Bunza ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 2026, a yau, 3 ga watan Agustan 2026,” in ji sanarwar.
“Iyalinsa da Ma’aikatar Shari’a ta jihar Kebbi sun tabbatar da sakin nasan. Duk da cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi kuɗin fansa, rundunar tana ci gaba da matsayarta mai ƙarfi ta ƙin biyan kudin fansa.
“A yanzu da aka sake alƙalin, ‘yansanda da sauran jami’an tsaro sun zafafa ƙoƙarin bincike na neman waɗanda suka aikata wannan aika-aikar tare da hukunta su.
“Rundunar na kira ga jama’a su ba da bayanai masu amfani da za su iya taimakawa a kan wannan. Dukkan bayanai da aka bayar za a yi amfani da su ba tare da bayyana waɗanda suka ba da bayanan ba.”

















