Yaƙin da Amurka ta ƙaddamar kan Iran da kuma martanin da Tehran ta mayar wanda ya haɗa da rufe Mashigar ruwa ta Hormuz ya janyo wa tattalin arzikin ƙasashen Larabawa asarar kusan dala biliyan 150 a cikin watan farko kaɗai (kimanin kashi 4 cikin 100 na jimillar kayayyaki da yankin ke samarwa, ko kuma kuɗaɗen shigar yankin na GDP), kamar yadda wata sanarwa daga hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana wa TRT World.
Sanarwar na daga cikin wani ɓangare na jawabin da Rania Al-Mashat, Mataimakiyar Sakatare-Janar na MDD kuma Sakatariyar Zartarwa ta ƙungiyar Tattalin Arziki da Zamantakewa ta Yammacin Asiya (ESCWA), ta gabatar a ranar Alhamis yayin wani taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasar Bahrain ta shirya.
“Bari na ambaci wani gagarumin adadi a nan. Bisa ƙididdigar ESCWA, kuɗaɗen da wannan rikici ya laƙume a watan farko kaɗai sun kai dala biliyan 150, wanda ya yi daidai da kashi huɗu cikin ɗari na jimillar tattalin arzikin yankin,” in ji Al-Mashat.
Ƙungiyar ESCWA ta ƙunshi ƙasashen Larabawa mambobi guda 21, waɗanda suka kama daga yankin Arewacin Afirka zuwa Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta haɗa kai da Isra’ila wajen kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu.
Hare-haren farkon yaƙin sun yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Addini na ƙasar Iran, Ali Khamenei, da kuma manyan shugabannin soji da na siyasa na ƙasar, tare da fararen-hula da dama — waɗanda da yawa daga cikinsu mata da yara ne.
Yanzu haka, wani bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya ke goyon baya ya bayyana cewa Washington ta aikata laifukan yaƙi a Iran yayin hare-haren farko na yaƙin.
Iran ta mayar da martani nan-take, inda ta ƙwace iko da Mashigar ruwan Hormuz mai muhimmanci — wadda ta nan ne kashi ɗaya cikin biyar na man fetur na duniya ke bi — tare da ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa kan ƙasashen Larabawa na yankin Gulf waɗanda ke ƙawance da Amurka, lamarin da ya taɓa ƙima da kwanciyar hankalin ƙasashen masu arzikin man fetur.
Al-Mashat ta shaida wa taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya wanda aka yi wa take da “Tekuna Masu Tsaro, Tsaro na Bai-Ɗaya: Kare ‘Yancin Ruwa a cikin Yanayin Tsaro Mai Canzawa” cewa barazanar da ke fuskantar harkokin jigilar ruwa a Hanyar tekun Hormuz da Bab al-Mandeb ba batun tsaro kaɗai ba ne; yana kuma kawo cikas ga ayyukan ci gaba da samar da muhimman kayayyaki da kwanciyar hankali na tattalin arziki da na ƙananan sana’o’i da kuma tattalin arzikin duniya baki ɗaya.
Ta ce Mashigar Hormuz na ɗaukar kusan kashi 25 cikin 100 na man da duniya ke amfani wanda ake wucewa da shi ta hanyar Tekun, da kuma kashi 19 cikin 100 na Iskar gas, kuma ta yi ƙara da cewa ƙasashen GCC suna fitar da babban kaso na albarkatun ammonia da taki da sulfur da kuma ma’adanin aluminum na duniya.
Ta shaida wa wakilan cewa kafin soma yaƙin Amurka da Iran, ƙasashen Larabawa 9 daga cikin 22 sun riga sun shiga ko kuma sun fito daga rikici, inda suke fama da lalacewar ababen more rayuwa da ƙarancin kuɗaɗe, tare da dogaro da abinci da mai da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Ta kuma ce tattalin arzikin yankunan ya yi ƙoƙarin haɓaka tsarin tattalin arzikinsu, sai dai yaƙin na janyo tsaiko na saka hannun-jari.
‘Ginshiƙai uku masu haɗe da juna’
Jami’ar ESCWA ta bayyana hanyoyin jiragen ruwa masu aminci a matsayin wani batu na ci gaba da tsaro, ba wai kawai batu na ƙarfin soja ba.
Al-Mashat ta yi kira da a ɗauki matakai masu inganci don magance rikicin da ake ciki bisa ga “ginshiƙai uku masu haɗe da juna.”
“Na farko, kare ‘yancin wucewa tare da tabbatar da tsaron jiragen ruwa na farar-hula da na kasuwanci da kuma tsaron hanyoyin jiragen ruwa bisa ga dokokin ƙasa da ƙasa,” in ji ta.
Kazalika ta yi kira da a hana bazuwar rikicin da kuma daƙile illolin da ke tattare da shi a kan iyakokin ƙasa, “ta haka za a rage tasirinsa a fannin tattalin arziki da zamantakewa da kuma jinƙai.”
Sakatariyar zartarwar ta ESCWA ta kuma yi kira da a ƙarfafa shirye-shiryen yankuna da juriyarsu don kare kayayyaki da kuma tabbatar da ci-gaban ayyuka.

















