Gabas Ta Tsakiya

Trump ya ce an shirya tattauna ta kai-tsaye tsakanin tawagogin Amurka da Iran, amma Iran ta musanta

Washington da Tehran sun ce za su aika tawagogi zuwa Doha, amma sun fitar da bayanai masu karo da juna, ciki har da lokaci da kuma dalilin tafiyar.

Newstimehub

Newstimehub

30 Jun, 2026

2026 06 21t113309z 1170972101 rc26yla3o0qb rtrmadp 3 iran crisis 1 2

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Iran ta nemi a tattauna ranar Talata a Qatar, duk da cewa Tehran ta musanta cewa an shirya tattaunawa da Washington kai-tsaye don cim ma yarjejeniya da nufin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Yarjejeniyar ƙasashen biyu ta farko kan dakatar da yaƙin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz ta yi ta gamuwa da tarnaƙi da iƙirarin da ke karo da juna daga ɓangarorin biyu.

Jim kadan bayan saƙon Trump na tabbatar da ganawar da Iran a Doha wadda ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Litinin, mai magana da yawunsa ya shaida wa tashar Fox News cewa wakilin Amurka Steve Witkoff da mai ba Trump shawara kuma surukinsa, Jared Kushner, “za su tashi zuwa Doha don halartar manyan tarurruka a wannan makon”.

Da safiyar Talata, CNN ta ruwaito cewa Witkoff yana kan hanyarsa ta zuwa Qatar.

Ko da yake, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya faɗa ranar Litinin cewa tawagar ƙwararrun ƙasar za ta je Doha a wannan makon, amma ya musanta duk wani zama da Amurkawa.

“Ba mu shiga matakin tattaunawa kan yarjejeniya ta ƙarshe ba tukuna,” in ji shi, yana mai cewa “a cikin kwanaki masu zuwa, ba za mu yi wani taron tattaunawa da ɓangaren Amurka a kowane mataki ba”.

Tattaunawa kan Hormuz

Batun ikon Iran kan Mashigin Hormuz mai matuƙar muhimmanci ya janyo tashin hankali a lokuta da dama. Na baya-bayan nan shi ne wanda ya faru a safiyar Lahadi, inda rundunar sojin Amurka ta ce ta kai hari kan wuraren soji 10 na Iran saboda zargin “ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci”.

Tehran ta ce ta mayar da martani da hare-hare kan sansanonin Amurka a Kuwait da Bahrain. Rufe mashigar na ci gaba da zama muhimmin batu a yarjejeniyar.

Iran da Oman suna iyaka da mashigar tekun, wadda kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas na duniya ke wucewa kafin rikicin. Sannan Tehran ta ce ranar Litinin sun gudanar da tattaunawarsu ta farko tun bayan da aka cim ma yarjejeniyar.

“A yayin wata tafiya zuwa Muscat, an gudanar da taron farko na Kwamitin Haɗin Gwiwa kan Hormuz,” kamar yanda Mataimakin Ministan Harkokin Waje na Iran, Kazem Gharibabadi ya bayyana a shafinsa na X.

Mashigar ta haɗa ruwan Oman da Iran, amma a ƙarƙashin dokokin ƙasa-da-ƙasa, ƙasashen biyu ba su da ikon rufe hanyar ko karɓar kuɗin shiga.

Iran ta yi gargaɗi a ranar Lahadi cewa, duk wani yunƙuri da jiragen ruwa za su yi na raɓawa ta hanyar ruwan Hormuz zai “ƙara tashin hankali” a Gabas ta Tsakiya.

Domin a cewar Iran, jigaren da ke ratsawa ta mashigar suna bi ta wata hanya ce da ke kusa da gaɓar tekunta.

Har yanzu dai ba a fayyace yadda za a aiwatar da yarjejeniyar ba, inda Tehran ta fi mayar da hankali kan batun haƙo ma’adinai.

A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa bayan taron da aka yi tsakanin Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Sultan Haitham bin Tariq na ƙasar Oman, shugabannin biyu sun ce za su gudanar da ayyukan haƙo ma’adinai tare.

A martanin da Iran ta mayar, Gharibabadi ya dage kan cewa a ƙarƙashin yarjejeniyar, Iran ce kawai take da ikon gudanar da ayyukan haƙo ma’adinai a wajen.

“Yanayin yana da matuƙar rikitarwa kuma yana da sarƙaƙiya. Muna bai wa Faransa shawara sosai da kada ta ƙara tsananta shi da abubuwan da ka iya ta da zaune tsaye,” kamar yadda Gharibabadi ya rubuta.

An samu cunkoson jirage a mashigar

A ƙarshen mako, an samu cunkoson jiragen ruwa bayan da aka buge wani jirgi yayin da yake ƙoƙarin ratsawa ta hanyar, inda a ranar Asabar jiragen 29 na kayayyaki suka ratsa. Sai kuma 12 kacal a ranar Lahadi, a cewar bayanai daga kamfanin bin diddigin ayyukan jiragen ruwa na Kpler.

Babu wani jirgin ruwa da ya bi ta hanyar kudu wadda ta ratsa ta ruwan Oman a cewar bayanan Kpler, yayin da wani rahoton na AXSMarine, ya gano cewa jiragen ruwa 44 sun daina aiki.

Yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma tsakanin Amurka da Iran wadda aka sanar a wannan watan, ta ce Iran ce za ta ayyana tsarin gudanarwa a nan gaba a tattaunawarta da Oman da sauran ƙasashen yankin Gulf, kuma dole hakan “ya yi daidai” da dokokin duniya.

Dakarun kare juyin juya halin Iran, sun ce suna ɗaukar matakai don taƙaita cunkoson jirage a hanyar mashigar, kuma za a hukunta jiragen ruwan da suka karya waɗannan matakan fiye da lokutan baya.

Mai ba da shawara ga jagoran addini na Iran, Mohammad Mokhber, ya rubuta a shafinsa na X cewa muddin Iran ce take gudanar da tsare-tsare a mashigar, “mafarkin ikon Washington a yankin ba zai taɓa cika ba”.