Nijeriya

‘Yanta’addan Boko Haram sun kai hari makaranta sun kashe malami tare da sace dalibai a Jihar Borno

Sun yi ta buɗe wuta , inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba

Newstimehub

Newstimehub

29 Jun, 2026

nigeria protest 86564

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta ƙaddamar da aikin neman wasu ɗailbai da da ‘yantaddan Boko Haram suka sace su yayin da suke rubuta jarabawarsu ta kammala karatun sakandare, NECO a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar ranar Litinin.

‘Yanta’addan na Boko Haram sun isa makarantar gwamnati ta GDSS da ke Lassa, a ƙaramar hukumar Askira/Uba sanye da kayan sojin boge da kuma kayayyakin jami’an tsaron soji, domin yaudarar mutane cewa su jami’an tsaro ne, kamar yadda ‘yansanda da mazauna wurin suka sanar da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Sun buɗe wuta, inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su sace ɗaliban da ba a san adadinsu ba.

‘Yanta’addan riƙe da muggan makamai sun danna cikin makarantar ne da safiya , inda suka yi ta harbi kafin su tafi da ɗaliban.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Borno Nahum Daso ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa an tura jami’an tsaro domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su da kuma kamo maharan.

“Da misalin ƙarfe 9 na safe (na ƙasar), ‘yantadda sun kai hari makarantar sakandare ta jeka ka dawo ta Lassa. Sun yi ta harbi nan da can. An saci ɗalibai da dama ,” kamar yadda Daso ya shaida wa Anadolu ta waya.

Ya ƙara da cewa dakarun tsaro sun yi arangama da maharan kuma kwamishinan ‘yansanda ya nemi kwamandan ‘yansanda na yankin ya jagoranci aikin da ake yi a yanzu.

“A halin yanzu suna neman ceto waɗanda aka yi garkuwa da su,” a cewar Daso, ba tare da ba da haƙiƙanin adadin ɗaliban ba.

Garkuwa da mutane na baya-bayan nan ya faru ne cikin rashin tsaro da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a arewa maso gabashin ƙasar duk da shekaru da aka shafe na ayyukan soji a kan Boko Haram da ɓangaren da ya ɓalle daga gareta, ISWAP.

Ƙungiyoyin ‘yantadda sun yi ta kai hare-hare kan makaranti a yankin arewacin ƙasar , lamarin da ke haddasa garkuwa da mutane da yawa irin na ƙaurin sunan da suka yi wajen garkuwa da ‘yanmatan Chibok a shekarar 2014 a jihar Borno.

Harin na ranar Litinin na zuwa ne makonni bayan ‘yanta’adda sun yi garkuwa da fiye da ɗalibai da malamai 40 daga makaranti uku a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo dake kudu maso yammacin ƙasar .

Lamarin ya haddasa zanga-zangar ƙungiyoyin ƙwadago da masu fafatukar kare haƙƙin bil’adama da ɗalibai a faɗin ƙasar da kuma sabunta damuwa game da amincin makaranti a faɗin Nijeriya.