Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu

Gidan taladijin ɗin ya ambato wata sanarwar daga ma’aikatar na cewa ambassada Ali-Gombe ya miƙa saƙon gaisuwar Shugaba Tinubu yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta duƙufa ga kare ‘yan Nijeriya a ketare.

Newstimehub

Newstimehub

30 Jun, 2026

fde00c19c0deb8628d7f55b8e3e0e07621d790463686745cb6a757e855035320

Gwammatin Tarayyar Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga ƙasar Afirka ta Kudu tana mai alƙawarin kare ‘yan ƙasar da ke zaune a ƙetare.

Gidan tabalijin na ƙasar NTA ya ruwaito cewar mutanen da suka sauka a filin jirage sama na Murtala Mohammed da ke sun samu tarbar daraktan da ke kula da lammuran Afirka a ma’ikatar ƙasashen wajen Nijeriya, ambassada Haruna Ali-Gombe, wanda ya gabatar da jawabin Shugaba Tinubu na tabbacin kare ‘yan Nijeriya a ƙetare.

Gidan taladijin ɗin ya ambato wata sanarwar daga ma’aikatar na cewa Ambassada Ali-Gombe ya miƙa saƙon gaisuwar Shugaba Tinubu yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta duƙufa ga kare ‘yan Nijeriya a ketare.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan shi ne jirgi na biyu da ke kuɓutar da ‘yan Nijeriya daga ƙasar, lamarin da ya mayar da adadin waɗanda suka koma Nijeriya daga Afirka Ta Kudu 335 cikin wa’adin ranar 30 ga watan Yunin da aka bai wa ƙetare su bar Afirka ta Kudu.

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin Afirka Ta Kudu domin tabbatar da aminciun ‘yan Nijeriya da ke zama a wurin duk da cewa tsarin kuɓutar da mutane da raɗin kansu yana gudana yayin da ake sauraron ƙarin sauƙar jirage a a ƙasar a cikin ‘yan kwanakin nan domin tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriyar da aka rika aka tantance su sun dawo ƙasar da raɗin kansu.

Baƙi dai a Afirka ta Kudu suna fuskantar matsi daga ‘yan ƙasar da ke ganin cewa baƙin suna karɓar ayyukan da ya kamata ‘yanƙasa ne suke yin su.

Wannan na faruwa ne yayin da adadin matasa mara sa ayyukanyi a ƙasar ya kai kashi 46 cikin 100.