Shugaba Bola Tinubu ya bayyana sake zaɓen gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun a matsayin wata alama cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Nijeriya.
Shugaban wanda ya bayyana wannan a wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ya ce shi ya taya gwamnan murna a wata tattaunawar da suka yi ta wayar salula.
Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord (A) ya ci galaba kan Bola Oyebamiji na jam’iyyar APC da Najeem Salam na jam’iyyar ADC.
Ademola ya samu ƙuri’u 511,067 inda Oyebamiji ya samu 444,815 yayin da Salam ya samu ƙuri’u 17, 180.
“Sake zaɓen Gwamna Ademola Adeleke a zaɓen da aka kamalla na Osun wani tabbaci ne cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a ƙasarmu a ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC,” kamar yadda Tinubu ya bayyana a saƙon.
“ Na kira Gwamna Ademola Adeleke daga farko a yau domin na taya shi murna bisa nasarar zaɓensa a jihar Osun. Nasararsa ta sake tabbatar da ƙarfin gwiwar mutanen jihar Osun ke da shi game da shi. Ina masa fatan gagarumar nasarar yayin da yake shirin jagorantar jihar a cikin shekaru huɗu masu zuwa,” in ji shi.
“Yanzu da ya yi nasara, dole Gwamna Adeleke ya haɗa kan mutanen jihar ya kuma jagorance su ga ci-gaba da zaman lafiya da ci-gaba na zamantakewa da tattalin arziki ba tare da la’akari da abin da suka zaɓa a fannin siyasa a lokacin zaɓen ba,” in ji shi.
Ya yaba wa ƙarfin hali da kamun kai da dukkan ‘yantakaran suka nuna a lokacin zaɓen, yana mai cewa sakamakon zaɓen na wakiltar muradin mutanen jihar ne.
Shugaban ya kuma yaba wa hukumar zaɓe INEC da hukumomin tsaro bisa gudanar da “wani zaɓe na lumana da gaskiya wanda ya samar da wanda ya yi nasara ƙarara.”
Daga farko dai Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana a wani jawabin da ya yi bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaɓen cewa shugaban ƙasar ya kira shi domin taya shi murna bisa nasararsa.
Gwamnan ya yaba wa shugaban ƙasar bisa ba da dama a gudanar da zaɓe na gaskiya a cikin jihar, yana mai ƙarawa da cewa shi yana goyon bayan shugaban ya koma ƙaragar mulki a wa’adi na biyu.

















