Dakarun Hadin Gwiwa a Arewa Maso-Yamma, Farmakan FANSAN YAMMA sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su tare da kassara ‘yan ta’adda biyu a jihohin Katsina da Kebbi.
Dakarun sun kuma kama wasu mutum biyu da ake zargin ‘yanta’adda a farmakai daban-daban da aka kai a jihohin.
Jami’in Watsa Labarai na Dakarun Hadin Gwiwa a Arewa Maso-Yamma, Farmakan FANSAN YAMMA Laftanal Kanal Aliyu Danja ne ya bayyana cigaban a wata sanarwa a ranar 16 ga Satumba.
Sanarwar ta ce farmakan da aka kai a ranakun 14 da 15 ga Satumba sun kai ga kwato makamai, babur, kayan sarki da sauran kayayyaki.
A jihar Katsina, sojojin Sashe na 2 sun ceto mutane 10—ciki har da maza uku da mata bakwai—bayan sun amsa kiran gaggawa game da sace mutane daga unguwannin Unguwan Daudu da Unguwan Chibauna a Karamar Hukumar Funtua a ranar 14 ga watan Satumba.
Sojojin sun bi sahun masu garkuwar tare da yin musayar wuta da su, lamarin da ya kai ga ceto wadanda aka sace din, ciki har da wani jariri.
An kai wadanda aka ceton zuwa wurin sojoji domin daukar matakan da suka kamata.
A wannan rana kuma, sojoji a jihar Kebbi sun amsa kiran gaggawa bayan sace fararen hula daga kauyen Fafala da ke Karamar Hukumar Kangiwa.
Sanarwar ta kara da cewa, bisa dogaro da ingantattun bayanai na sirri, sojojin sun gudanar da sintirin yaki zuwa yankunan Fafala da Dandikwa, inda suka yi tsananin musayar wuta da ‘yan ta’addar, har hakan ya tilasta musu janyewa.
Bayan haka, farmakin da aka kai a yankin ya kai ga ceto mutane 21 da da aka yi garkuwa da su, wadanda aka sake hada su da iyalansu cikin nasara.
Kazalika, a ranar 15 ga Satumba, sojoji a Jihar Katsina sun dakile wani shirin da ‘yan ta’adda ke yi na kai hari kan al’ummomi a kananan hukumomin Matazu da Kankara.
Sojojin, wadanda suka yi aiki bisa ga bayanan sirri, sun yi tattaki zuwa maboyar ‘yan ta’addar, suka kuma yi musu luguden wuta mai karfi, inda suka kashe ‘yan ta’adda biyu, ciki har da Abbah Alhassan, wanda sojoji suka bayyana a matsayin wani sanannen dan ta’adda.
An rawaito cewa wasu ‘yan ta’adda sun gudu zuwa cikin dajin yankin
Kayayyakin da aka samu daga yankin sun hada da harsashai 10, babur, adda, kayan kariya, da tabar wiwi da sauransu.
A wani samame na daban a ranar, sojoji sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da ta’addanci a yankin Yantumaki na karamar hukumar Dan Musa da ke jihar Katsina.
Tambayoyin farko, a cewar sojoji, sun nuna cewa wadanda ake zargin suna da alaka da wani babban danta’adda da ake kira Mannori.
A halin yanzu wadanda ake zargin suna tsare don ci gaba da bincike.
Rundunar ta ce ayyukan sun jaddada ci gaba da kokarin da take yi na ceto wadanda aka sace, da wargaza hanyoyin sadarwa na ta’addanci, da kuma hana ‘yan ta’adda yin katabus a duk fadin yankin da take gudanar da ayyukanta na hadin gwiwa.
Ta yaba wa jama’a kan goyon bayan da suke bayarwa, inda ta kuma bukaci su ci gaba da taka tsantsan tare da kai rahoton ayyukan da ake zargi ga hukumar tsaro mafi kusa.

















